Sifetan Dan Sanda Ya Rasa Ransa Yayin Wani Mummunan Hatsarin Mota, Jami'ai Fiye da 10 Sun Jikkata

Sifetan Dan Sanda Ya Rasa Ransa Yayin Wani Mummunan Hatsarin Mota, Jami'ai Fiye da 10 Sun Jikkata

  • Wani mummunan hatsarin mota da ya afku a jihar Kebbi ya yi ajalin sifetan dan sanda, Saidu Idiya da jikkata wasu da dama
  • Hatsarin ya afku ne yayin da motar jami’an ‘yan sandan ta debo jami’ai masu binciken laifuka a kan hanyar Koko zuwa Jega a jihar
  • Nafiu Abubakar, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar ya tabbatar da faruwar hatsarin motar a jiya Lahadi 26 ga watan Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kebbi – Sifetan dan sanda mai suna Saidu Idiya ya rasa ransa yayin wani mummunan hatsarin mota da ya afku a jihar Kebbi.

Hatsarin ya afku ne yayin da motar jami’an ‘yan sandan ta debo jami’ai masu binciken lafuka a kan hanyar Koko zuwa Jega a jihar.

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri, Tinubu na da shirin ciyar da kasar nan gaba, shawarin minista ga 'yan Najeriya

Sifetan dan sanda ya mutu a wani mummunan hatsarin mota a Kebbi
Mummunan hatsarin mota ya yi ajalin dan sanda a jihar Kebbi. Hoto: Legit.
Asali: Twitter

Yaushe hatsarin ya afku a Kebbi?

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Nafiu Abubakar ya tabbatar da faruwar hatsarin motar a jiya Lahadi 26 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nafiu ya ce hatsarin ya afku ne bayan tayar mota kirar ‘Toyota Land Cruiser’ ta fashe tare da jifa da motar cikin daji, cewar Vanguard.

Ya ce motar ‘yan sandan na dauke da jami’ai guda 10 ne kan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Kooko/Besse yayin wani bincike.

Ya ce:

“A ranar 25 ga watan Nuwamba da misalin karfe 10 an samu mummunan hatsarin mota a kan hanyar Koko zuwa Jega a jihar Kebbi.
“Motar ‘yan sandan na dauke da jami’anta guda 10 yayin tafiya kauyen Kendawa da ke karamar hukumar Koko/Besse don gudanar da wani bincike.”

Mene 'yan sanda su ka ce kan marigayin?

Kara karanta wannan

Subhanallahi: Rayukan mutum 8 sun salwanta a wani mummunan hatsarin mota

Dukkan wadanda ke cikin motar an kwashe su zuwa asibitin Koko inda sifetan dan sanda Saidu Idiya ya rasa rayuwarsa a asibitin.

Daga bisani an dauki gawar Saidu da sauran wadanda su ka jikkata zuwa babban asibitin Gwamnatin Tarayya da ke birnin Kebbi.

Tuni aka binne marigayin dan sandan, Saidu Idiya kamar yadda addinin Musulunci ya karantar, cewar Punch.

Kakakin rundunar a karshe ya yi addu’a ga mamacin inda ya yi masa fatan samun rahamar ubangiji, cewar Daily Post.

Hatsarin mota ya lakuma rayukan ‘yan SDP 10

A wani labarin, wani mummunan hatsarin mota ya yi ajalin wasu magoya bayan jam’iyyar SDP a jihar Kogi.

Magoyan bayan na kan hanyarsu ce ta zuwa taron siyasa bayan shan kaye a zaben gwamna da aka gudanar a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.