Miji Ya Zargi Surukinsa Hakimi, Basarake a Kano da Kashe Masa Aure Tare da Yunkurin Tozarta Shi

Miji Ya Zargi Surukinsa Hakimi, Basarake a Kano da Kashe Masa Aure Tare da Yunkurin Tozarta Shi

  • Kotun shari'ar Muslunci ta gimtse wani aure mai shekaru sama da 10 bayan da mata ta kai mijinta kara
  • Ana zargin cewa, matar ta kullaci mijin ne tun bayan da ya angwance da amaryarsa mata ta biyu a shekarar da ta gabata
  • Kishi na kaiwa ga mutuwar aure sau da dama a yankuna daban-daban na Najeriya, musamman wannan zamanin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jhar Kano - Wani lamari mai sarkakiya ya faru a jihar Kano, inda wani malamin jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya koka tare da zargin surukinsa da kasha masa aure.

Wasu takarfun gayyatar kotu sun bayyana bukatar ganin mijin, Aliyu Abdulrahman Aliyu a gaban kotun shari’ar Muslunci don tattauna abin da matarsa Amana Jaafar Muhammad ta gabatar na neman a tsinke igiyar aurensu.

Kara karanta wannan

Yadda faston da ke sayar da tikitin shiga aljanna ya gusar da hankulan yayanmu, ya raba mu

A karar mai lamba CV/645/23, an tura sammaci ga Aliyu ta ofishinsa na aiki da ke ABU, lamarin da ya bayyana a matsayin kokarin bata masa suna da kuma hada shi da shugabanninsa a wurin aiki.

Yadda kotu ta raba auren miji da mata kan an kara mata kishiya
Karin kishiya ya sa an raba aure a kotu | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’ar ABU ta yi martani

A martanin da jami’ar ta yi ta hannun shugaban tsagayar ilimin gine-gine, ta bayyana balo-balo cewa, bai kamata kotun ta tura sakon gayyata ga Aliyu ta adireshinsa na ofis ba.

Jami’ar ta kafa hujja da cewa, babu alakar rayuwar gidan Aliyu da aikinsa a jami’ar, don haka ta nemi kotu ta sake salo wajen aike wasikar sammacin ga Malam Aliyu.

Hakazalika, wasikar ta martani ga wasu daidakun mutane baya ga kotun, ciki kuwa har da Sarkin Gaya, Turakin Gaya kuma Hakimin Dawakin Kudu, Alh. Jaafar Muhammad Usman.

A tattaunawar Legit Hausa da Aliyu, mijin matar da ta yi kara, ya ce yana zargin hannun hakimin na Dawakin Kudu, wanda shi ne surukin nasa da tsoma baki da kuma tasiri wajen murda shari’ar.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 2 muhimmai da ya kamata ku sani yayin da ake yanke hukuncin shari'ar zaben Nasarawa

Lauyoyi sun yi magantu kan shari’ar

A wata tattaunawar manema labarai da lauyoyin wanda ake kara da wacce ta shigar da kara, sun bayyana yiwuwar samun sulhu a farko.

A cewar Umar Yusuf Khalil, lauyan Aliyu ya ce:

“Shi al’amarin aure, kamar yadda kowa ya sani, akan zauna kuma akan saba kuma matukar Allah bai kawo karshen al’amari ba babu yadda za a yi a ce an rabu."

Da yake amsa tambaya kan cewa ana zargin matar Aliyu ta shigar da kara ne saboda ya kara amarya, lauyan ya ce ai shari’a bata hana ba, don haka yana da kwarin gwiwar samun sulhu.

Lauyan mata ya magantu

Sai dai, Ibrahim Umar, lauyan matar da ta shigar da kara ya ce ba batu ne na kishin Karin amarya ne ya jawo batun neman raba auren ba, wata matsalarce dai daban.

Ya kuma yi tsokaci da cewa, mai daki shi ya san inda ke masa yoyo, don haka shari’a ce za ta tabbatar da abin da ya ce a gaba.

Kara karanta wannan

Matatar mai a Najeriya ya fara aiki, ya tace lita miliyan 600 na fetur, ya shirya goggaya

Kotu ta gimtse igiyar aure

A zaman kotun da aka yi a ranar Litinin 20 ga watan Nuwamba, majiya daga kotu ta shaida cewa, tuni alkali ya raba auren.

Da wakilin Legit ya tuntubi Aliyu don jin ta bakinsa, ya bayyana cewa:

“Ba a bani damar yin sulhu da matata ba, wacce muka haifi yara hudu. An raba auren raina bai so ba kuma ina zargin akwai bita da kulli a wannan al’amarin.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.