Sanusi II: Hanyar Da Buhari Ya Bi Wajen Rusa Darajar Naira Da Jawo Hauhawar Farashin Kayayyaki

Sanusi II: Hanyar Da Buhari Ya Bi Wajen Rusa Darajar Naira Da Jawo Hauhawar Farashin Kayayyaki

  • Muhammad Sanusi II ya halarci taron masana, ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki da kamfanin MTN Group ta shirya
  • A wajen ne aka ji tsohon gwamnan babban bankin ya yabi irin matakan da Yemi Cordoso yake dauka yanzu a bankin CBN
  • Babu abin da ya jawo naira ta rasa kima da darajarta da hauhawan farashi a ra’ayin Sanusi kamar cin bashi daga CBN

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Tsohon gwamnan babban banki na CBN, Muhammad Sanusi II ya yi karin haske kan halin da tattalin arzikin kasar nan yake ciki.

A ranar Laraba, Leadership ta rahoto Muhammad Sanusi II ya na alakanta matsalolin da ake ciki a yau da yadda aka rika tafiyar da bankin CBN.

Kara karanta wannan

Yadda aka yi garkuwa da ni bayan tashi aiki - ‘Dan Jaridan fadar Shugaban kasa

Sanusi II
Muhammadu Sanusi II ya yabi matakan CBN Hoto: @MSII_dynasty
Asali: Twitter

Illar tasa CBN a gaba da bashi

Masanin tattalin arzikin yake cewa bashin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta rika karba wajen CBN ya taimaka a wajen rusa darajar Naira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga karya kudin kasar da cin bashi daga hannun bankin na CBN ya yi, Sanusi II ya ce wannan ne ya jawo tashin farashin kaya a kasuwa.

Ana zargin cewa gwamnatin tarayya ta rika buga kudin da babu kimarsu, su ka rika yawo a lokacin Muhammadu Buhari ya na karagar mulki.

Sanusi II ya yabi Gwamnan CBN

An rahoto Sarkin Kano na 14 ya na cewa yanzu da CBN ya canza salon gudanawarsa, ya nuna an maida hankali a kan abin da ya fi kamata.

Sabon gwamnan da aka nada ya fito da tsare-tsare irinsu OBB domin yakar tashin farashi.

Kara karanta wannan

Ka Canza Hali: Tsohon Shugaba a APC Ya Fadi Kuskuren Tinubu Daga Shiga Aso Rock

Buhari ya yamutsa bankin CBN?

Sanusi II ya ce yana fatan abubuwa za su gyaru ba dadewa ba, bayan an yi shekaru takwas gwamnati ta na laftawa bankin CBN nauyi.

Mai martaba ya kara da cewa farashin kudin waje ya na daidaita, ana yin abin da ya kamata ta hanyar biyan bashi da sakin kudi a kasuwa.

Khalifa ya yi wadannan bayanai wajen taron da kamfanin MTN Group ya shirya da ya samu halartar ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki.

CBN zai bar tsofaffin N200, N500 da N1000

A jiya aka ji labari babban banki na CBN ya ce ba za ayi watsi da tsofaffin kudi ba domin an sha wahala a kokarin canza manyan takardun.

Sanarwar ta nuna babu ranar da za a daina amfani da tsofaffin N200, N500 da N1000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng