Buhari: Aron kudinmu ya na wuce abin da mu ke samu – Inji CBN

Buhari: Aron kudinmu ya na wuce abin da mu ke samu – Inji CBN

Gwamnan babban bankin Najeriya na CBN ya yi kira ga gwamnatin tarayya da babbar murya a game da yawan bashin da ke kan kasar a halin yanzu.

Shugaban CBN ya yi wannan kira ne a lokacin da aka yi wani zaman a kwamitin MPC na bankin a Ranar Juma’ar, 25 ga Watan Junairun 2020 a Garin Abuja.

A wannan zama wanda shi ne na 271 da aka yi, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa bashin kudin da ke kan wuyan gwamnatin Najeriya ya na kara tashi.

Mista Godwin Emefiele ya nunawa gwamnati cewa yawon kudin da ta ke arowa ya na kerewa abin da ta ke samu a cikin asusunta daga gida da kuma waje.

Bayan jan kunne game da karuwar bashin da gwamnati ta ke faman ci, gwamnan na babban banki ya yi magana game da tsarin kason gwamnati na FAAC.

KU KARANTA: Buhari ya amince da wasu nadin mukamai a CBN, NCAA da NCC

Buhari: Aron kudinmu ya na wuce abin da mu ke samu – Inji CBN
CBN sun ce cin bashin Najeriya ya haura abin da ta ke samu
Asali: Twitter

Emefiele ya yi gargadi game da rabawa gwamnatocin tarayya da na jihohi da kuma kananan hukumomi, gaba daya abin da aka samu daga arzikin mai.

Kwamitin na MPC ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta daina dogara kaco-kam daga kudin shiga, ya yi kira a maida hankali wajen fadada tattalin arziki.

Za a fadada tattalin arzikin kasar ne ta hanyar inganta tsarin karbar haraji a Najeriya a cewar wannan kwamiti da ke lura da yadda kudi ke yawo a kasa.

A karshe wannan kwamiti ya bada shawarar cewa Najeriya za ta habaka sosai muddin aka rage yawan kudin da ake batarwa wajen tafiyar da gwamnati.

Ministar kudi da kasafin Najeriya, Zainab Ahmed, ta na a kan ra’ayin cewa bashin Najeriya bai yi yawa ba, sai dai kasar na fama da matsalar karbar haraji.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng