Manyan Malaman Addinin Musulunci 5 Da Buhari Zai Baiwa Lambar Karramawa Yau

Manyan Malaman Addinin Musulunci 5 Da Buhari Zai Baiwa Lambar Karramawa Yau

Gwamnatin tarayya ta fara shirye-shiryen bikin raba lambobin karramawa ga wasu zab'bbun ‘Yan Najeriya bisa gudunmuwar da suka baiwa kasar.

Lambobin karramawar sun hada da na GCON, CFR, CON, OON, MFR dss.

Wadanda za a ba lambobin yabo sun hada da ‘yan siyasa, ma’aikata, jami’an tsaro, ‘yan kasuwa da wasu maluman addini.

Da cikin sama da mutum dari hudu da za'a baiwa lambar karramarwar, gwamnati ta gayyaci wasu Shehunnai taron dake gudana yanzu haka a farfajiyar International Conference Center ICC dake birnin tarayya Abuja.

Malamai
Manyan Malaman Addinin Musulunci 5 Da Buhari Zai Baiwa Lambar Karramawa Yau
Asali: Facebook

Ga abinda ya kamata ka sani a takaice game da Malaman addinin Musulunci 5 da za'a karrama

1. Farfesa Umar Sani Rijiyar Lemo, OON

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Farfesa Umar Sani Rijiyar Lemo Malami ne a tsangyar nazari da ilmin addinin musulunci a jami'ar Bayero dake jihar Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Za ta Karrama Mashahurin Malamin Musulunci, Sani Rijiyar Lemu

Shine shugaban cibiyar bincike da muhawarar addinai

2. Dr. Bashir Aliyu Umar, OON

Dr Bashir ne babban limanin Masallacin Al-Furqan dake Nasarawa GRA a jihar Kano.

3. Sheikh Muhammad Tajudeen Adigun, OON

Sheikh Tajudden shine babban limamin Masallacin Fouad Lababidi dake unguwar Wuse dake birnin tarayya Abuja. Hakazalika shine shugaban kwamitin limaman Abuja.

4. Imam Abdullahi Abubakar, MON

Imam Abdullahi limamin Masallaci ne a jihar Plateau wanda ya shahara da boye wasu mabiya addinin Kirista lokacin da rikici ya barke a yankinsa ana kokarin kashesu

5. Sheikh Suleiman Farouq Onikijipa, OON

Suleiman Farouq shine Muftin Lardin Ilori kuma jagoran kungiyar Al-Amaani a jihar Kwara.

Mufti
Manyan Malaman Addinin Musulunci 5 Da Buhari Zai Baiwa Lambar Karramawa Yau
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel