Cin hanci da rashawa na hau-hawa ne saboda ba a daure masu laifi, in ji Amaechi

Cin hanci da rashawa na hau-hawa ne saboda ba a daure masu laifi, in ji Amaechi

- Ministan sufuri na kasa ya bayyana dalilin da yasa cin hanci da rashawa yayi yawa

- Yace, rashin hukunta barayin da suka wadata kansu da kudin jama'a ne yake kara lamarin

- Ya kuma shawarci al'umma da su daina hada biki don girmama masu cin hanci da rashawa

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya fada a ranar Litinin cewa cin hanci da rashawa ya ci gaba a kasar ne saboda wadanda suka bayyana barayi ba a daure su ko kuma hukunta su, jaridar The Punch ta ruwaito.

Amaechi, wanda ya yi magana a lokacin da yake gabatar da lacca ta 2021 na Jami’ar Fatakwal, ya bukaci jama’a su daina yin bikin girmama mutanen da suka wadata kansu ta hanyar satar dukiyar jama’a.

KU KARANTA: Kungiyoyin Arewa suna marawa Gumi baya kan samar da filayen kiwo ta kasa

Cin hanci da rashawa na hau-hawa ne saboda ba a daure masu laifi, in ji Amaechi
Cin hanci da rashawa na hau-hawa ne saboda ba a daure masu laifi, in ji Amaechi Hoto: Naira Metrics
Asali: UGC

Ya kuma lura da cewa irin wadannan bukukuwa suna karfafa cin hanci da rashawa.

A cewarsa, “Har sai mun fara daure barayi, idan ba haka ba cin hanci da rashawa zai ci gaba; dalilin da ya sa cin hanci da rashawa yake karuwa saboda ba a hukunta masu laifin ne, ba a daure kowa ba.”

Tsohon gwamnan na jihar Ribas, ya ce mulkin shugaban kasa mai ci, Manjo Janar Muhammadu Buhari, ya kuduri aniyar yaki da cin hanci da rashawa kuma yana yin hakan ne a gaba.

KU KARANTA: Sabon shugaban sojoji ya sake ziyartar jihar Borno a karo na biyu

A wani labarin, Mista Umar Ndashacba, Manajan Shirye-shirye na Shirin Ciyar da Makarantun Gida na Kasa (NHGSFP) a Neja, ya ce aƙalla an samar da ayyuka sama da 14,000 a cikin shekaru biyu da kasancewar shirin a jihar.

Ndashacba ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.