Yan Bindiga Sun Salwantar da Ran Wata Mata da Jaririyarta a Sokoto

Yan Bindiga Sun Salwantar da Ran Wata Mata da Jaririyarta a Sokoto

  • Wata matar aure da ɗaya daga cikin tagwayen jariranta mata sun riga mu gidan gaskiya bayan ƴan bindiga sun buɗe wuta kan motar da su ke ciki
  • Matar dai ana kan hanyar kai ta asibiti ne domin ƙara mata bayan ta haihu a gida sannan ta zubar da jini sosai
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa direban motar, matar da ɗaya daga cikin tagwayen sun ƙone har lahira a cikin motar bayan ta kama da wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - An ƙona wata mata har lahira mai suna Sharifa Noma tare da ɗaya daga cikin ƴaƴanta tagwaye mata a wani harin ƴan bindiga a jihar Sokoto.

A cewar majiyoyi, matar ta haihu a gida da misalin ƙarfe 2:30 na daren ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Amarya ta cinnawa gidan mijinta wuta kan abu 1 a Adamawa

Yan bindiga sun yi silar rasuwar matar aure da jaririyarta
Yan bindigan sun bude wuta kan motar da ke dauke da matar da jariranta Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Zubar da jinin da ta yi mai yawa bayan haihuwarta ya sanya ƴan uwanta suka yanke shawarar kai ta asibiti domin a ƙara mata jini.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Sai dai, lokacin da su ke cikin tafiya a kan titin hanyar Ruwa wuri-Bugawa a ƙaramar hukumar Tangaza, motar su ta bugi wani shingen da ƴan bindiga suka sanya a kan hanyar.

Ƴan bindigan sun buɗe wuta kan motar inda ta ƙwace wa direban ya je ya bugi wata bishiya sannan ta kama da wuta.

Majiyar ta ƙara da cewa direban, matar da ɗaya daga cikin tagwayen sun ƙone ƙurmus a motar.

Wani mazaunin ƙauyen mai suna Kabiru ya bayyana cewa, sauran fasinjojin da suka haɗa da ɗayar jaririyar, sun tsira da raunuka kuma a halin yanzu suna jinya a asibiti.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun buɗe wuta, sun yi garkuwa da shugabar ƙaramar hukuma a jihar Arewa

Da aka tuntubi Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce ba zai iya tabbatar da aukuwar lamarin ba saboda ba a yi masa bayani ba.

Ya yi alkawarin zai kira waya da zarar ya samu bayani.

Ƴan Bindiga Sun Sungume Hakimi a Kaduna

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun yi awon gaba da hakimin Kujama a ƙaramar hukumar Chikun, Steven Ibrahim, a yayin wani hari.

An dauke Steven Ibrahim. Ne tare da wasu mutane biyu yayin da su ke fitowa daga wani wajen shaktawa da ke bayan makarantar Bethel Baptist.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng