Dan Majalisa a Kano Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Maganin Yarinya Yar Shekara 5 Mai Fama da Cutar Daji
- Honarabul Abdulmumin Jibrin Kofa ya yi alƙawarin biyan kuɗaɗen asibitin Fatima Shu’abu ƴar shekara biyar
- Yarinyar tana fama da cutar daji da ta cinye kusan rabin fuskarta kuma tana barazanar shafar idonta na dama
- Ɗan majalisar ya yi alkawarin kai ta kowane asibiti a Najeriya da ƙasar waje domin samun kulawar da ta dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Taimako ya zo wa Fatima Shu'aibu ƴar shekara biyar da ke fama da cutar daji a fuskarta yayin da Abdulmumin Jibrin Kofa, ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin biyan kuɗaɗen da za a duba lafiyarta.
Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bebeji/Kiru, a majalisar wakilai, ya bayyana hakan a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba.
A cewar wata sanarwa da mai taimaka wa Kofa kan harkokin yaɗa labarai, Sani Ibrahim Paki, ya fitar a shafin Instagram, ya ce cutar daji ta cinye kusan rabin fuskar Fatima ƴar shekara biyar kuma tana barazanar shafar idonta na dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane alƙawari ɗan majalisar ya yi?
Da yake magana da iyayen Fatima, Kofa ya yi alkawarin kai ta kowane asibiti a Najeriya da ƙasar waje domin samun kulawar da ta dace.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Ina da kyakkyawan tsari na tallafawa irin wannan a garinmu na Kofa da kewaye. Na kuma tabbatar na sanya hanyoyi masu sauƙi da yawa don isa gare ni. Lokacin da aka aiko min da saƙo game da wannan lamarin, na yi sauri na yi bincike na haɗu da yarinyar da iyayenta a yau."
"Iyayenta sun bayyana cewa ƙila wani da suka haɗu da shi a asibiti ya kai labarinta kafafen sada zumunta don neman taimako a gare su da kyakkyawar niyya. Mun gode masa akan hakan. Na karɓi lamarinta yanzu, kuma zan biya mata kuɗaɗenta gaba ɗaya kamar yadda na yi wa mutane da dama kuma har yanzu ina yin wasu da dama a halin yanzu.”
Ɗan majalisar ya kuma bayar da gudunmuwar wasu kuɗaɗe ga yarinyar domin taimaka wa iyayenta samun sauƙin zirga-zirga zuwa asibiti.
Malamin Jami'a a Arewa Ya Binciko Maganin Cutar Daji
A wani labarin kuma, wani malamin jami'a a Arewacin Najeriya ya binciko maganin cutar daji.
Farfesa Isa Marten Hussaini na jami'ar Maiduguri ya gudanar da bincike wanda ya gano maganin cutar daji ta hanyar amfani da magungunan gargajiya.
Asali: Legit.ng