Bincike ya bayyana yadda za a fayyace cutar daji tun kafin ta fara yaduwa a jikin dan Adam

Bincike ya bayyana yadda za a fayyace cutar daji tun kafin ta fara yaduwa a jikin dan Adam

A wani sabon bincike da aka gudanar a jami'ar John Hopkins dake kasar Amurka, ya bayyana yadda za a fayyace cutar daji ta hanyar gwajin jini tun kafin ta fara wani tasiri a jikin dan Adam

Wannan sabon bincike zai zamto juyin juya hali a duniya domin kuwa zai taimaka matuka wajen magance da yin rigakafin cutar ga ma su ita tun kafin ta fara wani tasiri.

Binciken, wanda aka buga a mujallar Science Translational Medicine, ya bayyana cewa, za a iya gano ciwon daji a mafi yawan mutanen da ke dauke da ita a mama, hanji , huhu, da ciwon daji na mahaifa.

Binciken ya gano ciwon daji a cikin jinin fiye da rabin masu cutar a mataki na farko da aka gwada, kuma anyi dacen gano cutar tun kafin ta fara bayyana a jikin mutanen.

Bincike ya bayyana yadda za a fayyace cutar daji tun kafin ta fara yaduwa a jikin dan Adam
Bincike ya bayyana yadda za a fayyace cutar daji tun kafin ta fara yaduwa a jikin dan Adam

An gano cutar dajin a kashi 45 cikin 100 na ma su dauke da cutar a huhu, kashi 67 na ma su dauke da ita a mahaifa, da kuma wani kashi 67 na ma su dauke da ita a mama, kuma dukansu sun kasance dauke da cutar tun kafin ta fara bayyana a jikin su.

Masu binciken sun tabbatar da cewa, akwai mutane 44 da aka gwada kuma binciken ya bayyana daidai domin kuwa ba sa dauke da cutar ta daji.

KU KARANTA: Akwai katin shaidar dan kasa fiye da 20, 000 da ba a karba ba - NIMC

Johns Hopkins da 'yan kungiyar sa, sun gano binciken ne ta wata hanya da ake kira 'targeted error correction sequencing'.

Sun binciki kaloli 58 na cutar ta hanyar amfani da jini kuma sun gano kwayoyin cutar da suke maye guraben jiki a sassa daban- daban.

Duk da wannan, kungiyar ta ce ana bukatar inganta hanyoyin gwajin domin samun daidaito da kuma bunkasa ikon gano cutar.

Wani likita Dakta Wyndham Wilson, na cibiyar binciken cutar daji ta duniya ya bayyana cewa, guje wa sakamakon da ba daidai ba yana da muhimmanci ga makomar gano ciwon daji, domin kuwa cutar daji a mataki na farko ta na iya bacewa wanda har yanzu ba gano dalilin bacewar ba.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng