Alhamdulillah: Wani fitaccen malamin jami’a a Arewa ya binciko maganain cutar daji
Farfesa Isa Marten Husseini na jami’ar Maiduguri wanda ya shahara a fagen ilimin sarrafa magungun ya lashe wata babbar lambar yabo daga cibiyar bincike da bada horo da cigaban tatttalin arziki (IITRED) sakamakon wani muhimmin bincike daya gudanar akan cutar Daji (Cancer).
Jaridar Yerwa Express ta ruwaito cibiyar ta yanke shawarar karrama Farfesa Isa ne sakamakon binciken da yayi wanda ya gano maganin cutar daji ta hanyar amfani da magungunan gargajiya, kamar yadda cibiyar ta bayyana.
KU KARANTA: EFCC na yunkurin maka tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari a Kotu
Majiyar Legit.com ta ruwaito za’a gudanar da bikin karramawar ne a ranar 15 ga watan Nuwamba na shekarar 2018 a dakin taro na babban Otal din alfarma Sheraton dake babban birnin tarayya Abuja.
Farfesa Isa ya yi namijin kokari wajen binciko maganin guda daga cikin cututtukan dake addabar jama’a da dama a Duniya tare da halakasu har lahira ta amfani da magungunan gargajiya, wanda hakan yasa dalibansa suke yi masa kirari da maganin cancer “Hope for cancer”.
Farfesan yace tun a shekarar 2010 ya fara gudanar da wannan bincike na gano maganin cutar daji, wanada a yanzu haka yace binciken ya kai wani matakin da za’a iya fara amfani dashi akan dabbobi, daga bisani kuma akan mutane.
“Dole ne sai mun fara amfani da maganin akan dabbobi, sa’annan mu yi amfani dasu akan mutane, wannan shine ake kira da suna gwajij magani, matakin karshe kafin a watsa maganin a kasuwa.” Inji shi.
Ana sa ran a yayin karrama farfesan, zai yi bayanin bincikensa da sakamakon daya samu ga mahalarta taron na mintuna goma sha biyar don su fahimci hanyoyin da ya bi wajen gudanar da wannan muhimmin aiki.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng