Cin ganyen ayayo na maganin cutar daji da jijiyoyin zuciya - Masanin abinci

Cin ganyen ayayo na maganin cutar daji da jijiyoyin zuciya - Masanin abinci

Olugbenga Jagun, wani kwararre a fannin sinadarai masu gina jiki a jami’ar koyarwa na Abuja, Gwagalada, ya bayyana cewa ganyen ayayo na iya hana kamuwa da cutar kansa da na jijiyoyin zuciya saboda suna dauke da sinadarai masu amfani.

Mista Jagun ya fadi hakan ne a hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Abuja.

Ganyen ayayo na daya daga cikin ganyayyakin da ake amfani dasu sosai a nahiyar Afrika, musamman a matsayin miya.

Ayayo na dauke da sinadarin vitamin C, B, K yana kuma sauke da sinadarin kara karfin jiki wat Calcium da kuma iron.

Shan ayayo na iya hana kansa da cutar jijiyoyin zuciya- Kwararre a fannin sinadari
Shan ayayo na iya hana kansa da cutar jijiyoyin zuciya- Kwararre a fannin sinadari
Asali: UGC

“Wadannan sinadarai na da matukar amfani ga jikinmu kamar rage hawan jini da kuma daidaita shi a wajen mata masu juna biyu."

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisar dattawa: Mutanen Borno na tare da Ndume – Jigon APC

Ya kara da cewa ayayo na hana matsalar rashin bayan gida saboda yana dauke da sinarin ‘fibre’ a ciki.

Mista Jagun ya kuma bayyana cewa ganyen na iya taimakawa mutumin da ke fama da matsalar yawan kitse a jiki saboda baya dauke da sinadarin sa kiba da kuma maiko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel