Dan Majalisar APC Ya Rantse da Allah, Ya Ce Zasu Tuhumi Tinubu Kan Yadda Aka Yi da Kuɗin Tallafi

Dan Majalisar APC Ya Rantse da Allah, Ya Ce Zasu Tuhumi Tinubu Kan Yadda Aka Yi da Kuɗin Tallafi

  • Ɗan majalisar tarayya na APC, Yusuf Gadgi, ya ce zasu tambayi Tinubu abin da aka yi da makudan kuɗin tallafin Fetur da ya cire
  • Ya ce yana goyon bayan cire tallafi amma akwai lokacin da zasu gurfanar da Gwamnati ta yi bayanin yadda kuɗin tallafin suka amfani talaka
  • A cewarsa, idan an cire tallafin ya kamata ƴan Najeriya su amfana ta hanyar gyara hanyoyi, makarantu da gina asibitoci

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mamban majalisar wakilan tarayya, Honorabul Yusuf Gadgi, ya lashi takobin tuhumar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi bayanin maƙudan kuɗin da aka tara bayan cire tallafin fetur.

Hon Yusuf Gadgi.
Zamu Binciki Shugaba Tinubu Kan Makudan Kuɗin da Aka Tara Daga Cire Tallafi, Gadgi Hoto: Hon Yusuf Gadgi
Asali: Facebook

Ɗan majalisar ya kasance mamban jam'iyyar APC kuma shi ne shugaban kwamitin rundunar sojin ruwa na majalisar wakilan tarayya ta 10, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

A karshe, Shugaba Tinubu ya Tsoma baki, ya faɗi matsayar Najeriya kan yakin Isra'ila da Falasɗinu

Honorabul Gadgi ya ce yana goyon bayan tuge tallafin mai amma hakan ba zai hana shi bin ba'asin yadda Gwamnati ta kashe tiriliyoyin Nairan da aka tara ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata hira da BBCC Hausa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gadgi ya ce:

"Ina ɗaya daga cikin ƴan Najeriya da ke son cire tallafin mai saboda sata ce kawai, zamba ne cikin aminci, tallafin nan wallahi ba talaka ake yi wa ba."
"A kwamitin da nake shugabanta a majalisar wakilan tarayya na san wani abu dangane da tallafin, wasu manyan Najeriya ne kawai suke amfani da sunan tallafi su sace kuɗin talakawa su gina kansu."
"Amma duk da ina son cire tallafin mai, akwai lokacin da zai zo da zan tambayi Asiwaju (Bola Tinubu) a madadin ƴan Najeriya game wannan kuɗin tallafin man da aka cire.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, An bayyana halin da tsohon Gwamnan babban Banki CBN ya shiga bayan hukuncin kotu

Makudan kuɗi muke sanya wa hannu a lokacin Buhari

Ɗan majalisar ya ƙara da cewa tun lokacin Gwamnatin Muhammadu Buhari su ke rattaba hannu kan tallafin na Tiriliyan ɗaya, shida har Naira Tiriliyan 10.

"Lokaci zai yi da zan tambayi Asiwaju menene aka yi da waɗan nan kuɗaɗen da mutane zasu gani, su san eh an cire tallafin mai. Wallahi lokaci zai kai mu gurfanar da Gwamnati a gaban mu ko mu tambaye su gaba da gaba."
"Zamu tambaye su menene kuka yi wa talakawan Najeriya, idan an cire tallafin mai, talaka ya ganshi a gyaran hanya, makarantu, gina sabbin asibitoci da kamfanoni."

- Yusuf Gadgi.

Jonathan ya nemi a dakatar da zabukan da ake yi bayan babɓan zaɓe

A wani rahoton kuma Jonathan, ya yi kira ga majalisar tarayya da ta fara aikin yadda za a dakatar da zaɓukan da ake yi ba tare da babban zaɓen ƙasa ba.

Ya yi wannan kira ne bayan ya kaɗa kuri'arsa a rumfar zaɓe ta 39, gunduma ta 13, Otuoke da ke ƙaramar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel