A Karshe, Shugaba Tinubu Ya Tsoma Baki, Ya Faɗi Matsayar Najeriya Kan Yakin Isra'ila da Falasɗinu
- Bola Ahmed Tinubu ya yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Isra'ila da Falasɗinu a Gaza
- Shugaban ƙasar ya buƙaci a koma teburin sulhu, a lalubo hanyar masalaha wajen kawo ƙarshen lamarin cikin gaggawa
- Ya kuma tabbatarwa masu zuba hannun jari cewa su zuba dukiyarsu a Najeriya cikin kwanciyar hankali domin akwai riba mai yawa
Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Riyadh, Saudi Arabia - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada kiran da Najeriya ta yi na tsagaita wuta cikin gaggawa da kuma lalubo hanyar sansanta rikicin Isra'ila da Falasdinu cikin lumana.
![Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Saudiyya. Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Saudiyya.](https://cdn.legit.ng/images/1120/481d09821a455605.jpeg?v=1)
Asali: Twitter
Tinubu ya yi wannan kira ne ranar Juma'a yayin da yake jawabi a wajen taron Saudiyya da nahiyar Afirka wanda ya gudana birnin Riyadh na kasar Saudiyya, Daily Trust ta ruwaito.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/d2e3f2ce220942af.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
NLC da TUC sun gamu da cikas, kotu ta hana Ƙungiyoyin kwadago tsunduma yajin aiki a Najeriya
Yadda yaƙi ya barke a Gaza
Yaƙi ya barke ne tun bayan lokacin da kungiyar Hamas ta kai farmaki cikin Isra'ila, inda ta kashe mutane 1,400 tare da tsare wasu 2400, a cewar jami'an Isra'ila.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan haka ne Isra'ila ta lashi takobin murƙushe Hamas, inda ta fara kai harin bama-bamai a Gaza, wanda ma'aikatar lafiya ta ce an kashe mutane 10,500 ciki harda ƙananan yara.
Sai dai ƙasashen duniya na ta kiraye-kirayen a tsagaita wuta, haka nan zanga-zanga ta yawaita don kawo ƙarshen yaƙin ciki harda wadda aka yi a karshen makon nan a Amurka.
Muna maraba da masu zuba hannun jari - Tinubu
Da yake jawabi a wurin taron, shugaba Tinubu ya tabbatar wa masu son zuba hannun jari cewa dukiyarsu na da cikakken tsaro a Najeriya.
Ya ƙara da cewa Najeriya a shirye take tsaf kan kowane irin kasuwanci kana ya basu tabbacin cewa zasu ci riba mai tarin yawa a ƙasar nan, NTA News ta ruwaito.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/1f13acbee6634944.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Isra'ila/Hamas: A karshe, Isra'ila ta ji korafe-korafe, ta fitar da sanarwa kan tsagaita wuta
Ɗan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar APC Ya Sha da Kyar
A wani rahoton kuma Ɗan takarar Gwamna a inuwar APC a zaben jihar Bayelsa, Mista Sylva, ya sha da kyar a Kotun ɗaukaka ƙara ana gobe zaɓe.
Kwamitin alkatan Kotun, ranar Jumu'a, ya yi watsi da sabuwar ƙarar da aka shigar ana neman hana Sylva takara.
Asali: Legit.ng