An kama ɗan shekara 55 da ƙoƙon kan ɗan adam hudu

An kama ɗan shekara 55 da ƙoƙon kan ɗan adam hudu

- Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta cafke wani tsoho mai shekara 55 da ake zargi da mallakar sassan dan adam

- An shigar da korafi ne a ofishin 'yan sanda a Ago Iyewa inda DPOn yankin ya jagoranci kama mai laifin

- Kwamishinan 'yan sandan jihar Edward Ajogun ya bada umarnin dawo da batun sashen binciken manyan laifuka SCID

Rundunar yan sandan jihar Ogun ta kama wani dan shekara 55, Yesiru Salisu da laifin mallakar sassan dan adam da suka hada da kokon kai guda hudu, busassun hannaye biyu da muka muƙi guda uku kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyayemi ya fitar, kama wanda ake zargin ya biyo bayan wani rahoto da aka shigar a ofishin yan sanda na Ago Iwoye.

An kama dan shekara 55 da kokon kan dan adam hudu
An kama dan shekara 55 da kokon kan dan adam hudu. Hoto daga @Channelstv
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Maina: Ƙungiyar matasan arewa ta yi tir da tsare Ndume

Mai magana da yawun rundunar ya bayyana cewa, rahotannin sun bayyana cewa an ga wanda ake zargin da jakar da ake zargin kayan sata ne, kuma da aka tambaye shi meye a jakar, sai ya yar da jakar ya gudu jeji.

"Lokacin da muka karbi korafin, DPOn Ago Iwoye, CSP Paul Omiwole ne ya jagoranci jami'an sa zuwa inda abin ya faru, suka kuma bude jakar sai ga sassa mutane a ciki," a cewar sa.

Oyayemi ya ce sun caje jejin da ya gudu kuma sun gano shi.

"Da aka matsa masa, wanda ake zargin ya bayyana cewa ya hako ne a makabartar kiristoci ta Oke Eri," a cewar sa.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Edward Ajogun ya bada umarnin dawo da batun sashen binciken manyan laifuka don fadada bincike.

A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: