Umar Ka'oje: Farfesan Najeriya Ya Mayar Da Fiye Da Miliyan 1 Da Aka Tura Masa Bisa Kuskure

Umar Ka'oje: Farfesan Najeriya Ya Mayar Da Fiye Da Miliyan 1 Da Aka Tura Masa Bisa Kuskure

  • Hukumar gudanarwar makarantar NDA ta yaba wa Farfesa Umar Ka'oje bisa dattakon da ya nuna na mayar da kudin da aka tura masa bisa kuskure
  • Kudaden da suka kai N1,153,953.36, an ce an tura wa malamin bayan karewar kwangilar koyarwarsa da babbar makarantar soji ta kasar
  • Kazalika, makarantar ta ce tana duba yiyuwar karrama malamin a lokacin da ya dace kan wannan halin kirkin da ya nuna, wanda ya zama abin koyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Zariya, jihar Kaduna - A ranar Larabar da ta gabata, kwamandan makarantar horas da sojoji ta Najeriya (NDA), Manjo Janar John-Ochefu Ochai, ya ziyarci jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya domin yabawa Farfesa Umar Ka’oje bisa mayar da sama da naira miliyan daya da aka tura masa bisa kuskure.

Kara karanta wannan

An nada Farfesa Mohammed matsayin sabon shugaban jami'ar FUT Minna

Kudaden da suka kai N1,153,953.36, an ce an tura wa malamin bayan karewar kwangilar koyarwarsa da babbar makarantar soji ta kasar.

Makarantar NDA, Umar Ka’oje
Makarantar horas da sojoji ta Najeria (NDA) ta jinjina wa Farfesa Umar Ka’oje bisa amanarsa Hoto: Nigerian Defence Academy (NDA)
Asali: UGC

Ziyarar da kwamandan ya kai jami’ar, kari ne kan wasikar yabo da makarantar NDA ta aike wa malamin. An aike masa da wasikar ne a ranar 11 ga watan Satumba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahanatu Lawal shugabar sashen nazarin kimiyyar siyasa da nazarin kasa da kasa ce ta tarbi kwamandan, a cewar rahoton jaridar The Nation.

Lawal ta ce, "Mutane kalilan ne a yau za su iya nuna jajircewar farfesa Ka'oje, wanda ya kamata mai irin wannan hali na kwarai a rinka yin koyi da shi."

Makarantar NDA ta yaba wa Farfesa Ka'oje

A nasa jawabin, kwamandan NDA ya ce ya zama wajibi ya bi bayan wasikar yabo da aka rubuta wa farfesan domin kara nuna godiya ga irin wannan halin dattako da malamin ya nuna.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli: Za a Gudanar da zanga-zangar kwana 30 har sai Tinubu ya yi murabus

A cewarsa, irin halin da Mista Ka'oje ya nuna ba kasafai ake samunsa a irin wannan yanayi da ake ciki.

Mista Ka'oje ya yi godiya

Kwamandan ya kuma mika godiyarsa ga sashen jami'ar na yadda ya kafa al’adar horar da shugabanninsu wajen kasance wa masu gaskiya da rikon amana.

A nasa jawabin, Mista Ka’oje ya yaba wa makarantar, yana mai cewa, “Shi ma kwamandan ya cancanci a yaba masa saboda kaunarsa da sanin gaskiya.”

Tsarin Dibar Dalibai Karo Na 76 - NDA

Legit ta ruwaito maku yadda rundunar sojin Najeriya ta sanar da daukar sabbin dalibai zuwa makarantar sojoji ta NDA kashi na 76.

Wannan na cikin wata sanarwa ce da rundunar ta wallafa a shafin Twitter a yau Asabar 28 ga watan Oktoba, Legit ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel