LABARI DA DUMI-DUMI: An gano gidan da ake cin zarafin ‘ya’ya mata da yara a Adamawa

LABARI DA DUMI-DUMI: An gano gidan da ake cin zarafin ‘ya’ya mata da yara a Adamawa

- An gano wani gidan da ake cin zarafin ‘ya’ya mata da yara a adamawa

- Ana zaton cewa Hajiya Fadimatu Buba Bindir, 'yar uwan sakataren gwamnatin jihar ta mallaki wannan gidan

- Al’umma sun bukaci a yi mata kamun gaggawa domin yanke mata hukuncin da ya dace da ita

Rahotannin daga jihar Adamawa sun nuna cewa an gano wani gida inda ake zargin ana safara da cin zarafin ‘ya’ya mata da yara.

Kamar yadda Legit.ng ta samu daga shafin Rariya , ana zaton cewa wannan gidan mallakar wata mai suna Hajiya Fadimatu Buba Bindir, wadda 'yar uwa ce ga sakataren gwamnatin jihar Adamawa. Adireshin gidan wannan matan shine No. 53, Njuwa Road, Yola, jihar Adamawa.

Al’ummar wannan garin sun bukaci a yi mata kamun gaggawa domin yanke mata hukuncin da ya dace da ita.

LABARI DA DUMI-DUMI: An gano gidan da ake cin zarafin ‘ya’ya mata da yara a Adamawa
Daya daga cikin 'ya'ya mata da ake cin zarafin su a gidan Hajiya Fadimatu Buba Bindir

An kuma bukaci kungiyar lauyoyi wato 'Lawyers & Volunteers of CATBAN Citizens Complaint Center’ wanda ke jihar da su tuntubi wannan lamba na Kwamrade Mustapha Atiku Ribadu 08036303797 domin karin bayani.

KU KARANTA: Ki ceci rayuwan dan ki – Aisha Yesufu ta shawarci Aisha Buhari

Al’ummar wannan yankin sun kuma bukaci jama’a da a tashi tsaye don ganin an magance matsalar cin zarafi a tsakanin masu hannu da shuni da talakawa a kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel