Gwamnatin Tinubu Za Ta Yi Rigimar Farko da Malaman Jami’a da ASUU a Kan Kudi

Gwamnatin Tinubu Za Ta Yi Rigimar Farko da Malaman Jami’a da ASUU a Kan Kudi

  • Akwai alamun cewa kungiyar malaman jami’a da aka fi sani da ASUU za ta gwabza da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
  • Gwamnatin tarayya ta dabbaka shirin karbar 40% na kudin shigan da jami’o’i da sauran manyan makarantu su ka samu
  • ASUU da shugabannin jami’a sun yi tir da tsarin da aka kawo, a cewarsu za a sake jefa makarantu a cikin tsaka mai wuya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Kungiyar ASUU ta malaman jami’a da Kwamitin shugabannin jami’o’in Najeriya sun soki shirin da gwamnatin tarayya ta kawo.

Yanzu kuma Gwamnatin tarayya za ta rika tatsar 40% a kudin shigan da jami’o’i su ka tara, Punch ta ce sam jami’o’i ba su gamsu da wannan ba.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisa za su yi binciken yadda ake saida Digiri kamar ruwan leda a Jami’a

Shugabannin jami’o’i na ganin hakan ba komai ba ne illa gwamnati na kokarin takalo su watanni bayan sun dawo daga dogon yajin aiki.

'Yan ASUU
Zanga-zangar ASUU Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ASUU ta yi Allah wadai da gwamnati

Shugaban kungiyar ASUU ta kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce matakin da gwamnatin kasar ta dauka abin ayi Allah-wadai da shi ne.

Farfesa Emmanuel Osodeke yake cewa babu wani kudi da jami’o’i ke samu illa kudin makarantar da ake karba a hannun dalibai a duk shekara.

Farfesan ya ce abin mamaki ne gwamnatin Najeriya ta sa ido a kan kudin da ake karba a kan katin zama ‘dan makaranta da kudin kama daki.

Sauran kudin da ASUU ta ce ake samu ba su wuce na rigar dakin gwaji, wanda duk ana yi wa dalibai rangwame domin su samu saukin karatu.

Jawabin shugaban kungiyar ASUU

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu Za Ta Kirkiro Sababbin ‘Yan Sanda Domin Gadin Ma’adanai

"Abin da mu ka gani kenan a lokacin da mu ke yaki cewa gwamnati ta dauki dawainiyar jami’o’i, ‘Yan Najeriya sun dauka ASUU ce matsalar.
Jami’o’i ba cibiyoyin tatsar kudi ba ne, saboda haka 40% na rangwamen da ake yi wa dalibai a dakuna, lafiya da riguna za a raba da gwamnati?
Idan hakan ta faru, kalubalen kudin da jamio’i su ke fuskanta zai kara muni saboda jami’a ba cibiyar samun riba ba ce, ba wurin samun kudi ba ne."

- Farfesa Emmanuel Osodeke

Leadership ta ce an amince a fara cirewa makarantu kudin da su ka tara, Kungiyar ASUU ta ce za ta nemi zama da Ministan ilmi da Akanta Janar.

ASUU v Gwamnatin Tinubu

Kwanakin baya aka ji labari kungiyar ASUU ta gargadi Mai girma Bola Tinubu kan kare-karen kudin jami'o'i a Najeriya ana tsakiyar tsadar rayuwa.

Kungiyar ta ce hakan barazana ce ga makomar kasar idan har matasa su ka daina neman ilmi saboda yadda gwamnati ta tsawwala kudin karatu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel