Bidiyon Wani Mutum da Ya Juye Galan Din Man Ja a Injin Mota Ya Girgiza Intanet

Bidiyon Wani Mutum da Ya Juye Galan Din Man Ja a Injin Mota Ya Girgiza Intanet

  • Bidiyon wani mutum da ya zuba man ja a injin din mota ya yadu kuma ya ba mutane da dama mamaki
  • A bidiyon, wanda ya yadu a TikTok, an gano inda mutumin ya yuje galan din man ja a injin din, wanda ke nuna yana so ya yi amfani da shi a matsayin man injin
  • Wasu mutane sun lura cewa man jan zai shafi injin din nan da yan watanni kuma cewa mai motar zai yi danasanin haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jama'a sun yi cece-kuce a kan wani bidiyon TikTok da ya yadu wanda ke nuna yadda aka yi amfani da man ja a madadin man injin din mota.

A cikin dan gajeren bidiyon, mutumin ya juye galan din man ja a cikin injin din motar a wani wuri da ke kama da wajen gyaran motoci.

Kara karanta wannan

Wata mata ta yi yaji bayan sun samu sabani da mijinta, ya je biko da tsinken tsire 2

Wani mutum ya juye manja a injin din mota
Bidiyon Wani Mutum da Ya Juye Galan Din Man Ja a Injin Mota Ya Girgiza Intanet Hoto: TikTok/@ricochoco25.
Asali: TikTok

A cikin bidiyon wanda shafin @ricochoco25 ya wallafa, mutumin ya juye man jan a cikin injin din kamar dai yadda ake zuba man injin.

Wau mutane sun koka kan ci gaban, sannan suka gaggauta bayyana illart da wannan ka iya yi wa motar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, wasu mutane sun bayyana cewa za su gwada a nasu motocin don gabin abun da zai faru da injin din.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Korlynse ya ce:

"Ina ganin nine mutum na gaba da zan yi amfani da man ja a motata kirar Toyota."

@Nas ya yi martani:

"Duk wanda ya yarda da wannan makanikin ya zuba man ja a motarsa zai kasance cikin hawaye nan da yan watanni kadan."

@PURPOSE ta ce:

"Yanzu man ja da muke amfani da shi wajen girka wakenmu hankali kwance zai yi tsada."

Kara karanta wannan

Jama’a sun yi cacar baki yayin da budurwa ta amarce da hoton ango da baya nan, bidiyon ya yadu

@Tradesmart ya ce:

"Zuwa dan lokaci zai sa karfen ya yi tsatsa saboda kasancewar ruwa."

Motar da ake tukawa ta bai-bai

A wani labarin, wani fasihin mutum mai suna Rick Sullivan ya kirkiro wata mota wanda ba a taba ganin irin ta ba. Wannan ya faru ne a kasar Amurka.

Legit.ng tace Rick Sullivan ya kera wata mota da take tafiya a bai-bai. Wannan mutumi da makaniki ne, yace motar ba za ta taba shiga kasuwa ba.

Kamar yadda muka samu rahoto a ranar Litinin, 8 ga watan Nuwamba, 2021, Mista Rick Sullivan ya shafe tsawon wata da watanni yana aikin wannan mota.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel