Wani Da Ya Karanci Injiniyanci Ya Sace Injin Mota Na N2m Daga Jami'a, Ya Sayar N30,000 A Kasuwa

Wani Da Ya Karanci Injiniyanci Ya Sace Injin Mota Na N2m Daga Jami'a, Ya Sayar N30,000 A Kasuwa

  • Jami'an tsaro a jami'ar Calabar sun kama wani da ke da digiri a bangaren injiya kan satar injin mota na N2m ya sayar N30,000
  • Augustine Bisong, shugaban jami'an tsaro jami'ar ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin ya kuma bayyana wasu mutane biyu da suka taimaka masa
  • Bisong ya kara da cewa sun gano wani dan kasuwa a wata fitacciyar kasuwan Calabar wanda ya siya injin daga hannun dalibin kuma suna zurfafa bincike

Calabar - An kama wani dalibi da ya kammala karatun digiri a bangaren karatun injiniya kan laifin satar injin mota kirar Toyota Hilux mallakar Jami'ar Calabar.

Wanda ake zargin da abokan harkallarsa sun sayar da injin motar na Naira miliyan 2 kan N30,000, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ware Makudan Miliyoyi, Ya Tallafawa Mutanen da Ambaliya Ta Shafa a Kano

Suspects Calabar
Injiya Mai Digiri Ya Sace Injin Mota Na N2m, Ya Sayar N30,000 Kacal. Hoto: The Eagle Online.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban jami'in tsaro na jami'an, Kyaftin Augustine Bisong (mai ritaya) ya shaidawa manema labarai a Calabar cewa tawagar tsaro na jami'ar ta kama wanda ake zargin tare da wasu abokan harkallarsa biyu.

Ya ce su ukun sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa kuma sun ce sun sayar da injin kan N30,000 kacal.

The Eagle Online ta rahoto Mista Bisong kara da cewa an siyo injin ne domin a maye gurbinsa da wani da ya lalace kafin aka sace shi daga ofishin makanikai na jami'ar, kimanin sati biyu da suka shude.

Mun gano wadanda suka yi satar da wanda ya siya kayan satar, Mista Bisong

Mista Bisong ya ce:

"Mun gano wanda ya siya da sauran wadanda suka taimaka aka fitar da injin daga harabar jami'ar.
"Kawo yanzu, mun kama mutum uku; muna bibiyan wasu da ake zargi da hannu wurin satar injin da lalata wasu kayan jami'a.

Kara karanta wannan

Shari'a: Mutane 3 da suka rayu a magarkama na tsawon shekarau, aka gano ba su da laifi

"Wadanda aka kama sun dade suna adabar mutane a jami'ar ta hanar satar batirin mota, wayoyi da lalata lantarki na titi ta hanyar cire batira."

Wanda ke siyan kayan satar dan kasuwa ne a shahararren kasuwan Calabar, in ji Mista Bisong.

Bidiyon Ɓarawo Ya Maƙale a Cikin Ramin Da Ya Haƙa Don Shiga Coci Ya Yi Sata

A wani rahoton, kun ji cewa an kama wani da ake zargi da kutse cikin ginin coci da niyyar yin sata bayan ya makale a wani ramin da ya kutsa ya shiga cikin ginin cocin.

Wanda ake zargin mai suna Agyasuo ya kutsa cikin wani cocin Katolika ne da ke Techimantia, Tano South a kasar Ghana, Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164