Karar Zabe da Shari’a 5 da Abba Gida Gida Ya Rasa a Wata 6 da Zama Gwamnan Kano
- A watan Satumba Abba Kabir Yusuf ya rasa shari’ar zaben Gwamnan Kano, Alkalan kotun korafin zabe su ka ba APC nasara
- Kotun tarayya ta takawa sabuwar Gwamnati burki, ta hana ayi bincike kan abubuwan da su ka faru a lokacin Abdullahi Ganduje
- Lauyoyin kungiyoyin ‘yan kasuwa da masu makarantun kudi sun fara samun galaba a kan Lauyoyin Gwamnatin Kano a kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Jihar Kano - Daga lokacin da Abba Kabir Yusuf ya zama Gwamnan jihar Kano a ranar 29 ga watan Mayun 2023, an yi ta gwabza shari’a da shi a kotu.
Rahoton nan ya dauko hukuncin shari’o’in da aka yi wanda aka yi nasara a kan Mai girma Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida Gida.
1. Abba ya rasa shari’ar zaben gwamnan Kano
A karkashin jagorancin Alkali Oluyemi Akintan-Osadebay, kotun sauraron karar zaben Gwamnan Kano a 2023 ta tsige Abba Kabir Yusuf na NNPP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta ce Nasiru Yusuf Gawuna ne halattaccen gwamna bayan soke kuri’u 165, 663 da NNPP ta samu, ta ce bai dace a kirga da wadannan kuri’u ba.
2. Abba Kabir Yusuf da ‘Yan kasuwa
Babban kotun tarayya mai zama a Kano ta ba gwamnati rashin gaskiya a shari’arta da ‘yan kasuwan masallacin idi da aka rusawa shagunansu.
Lauyan ‘yan kasuwan, Dr. Nuraddeen Ayagi ya yi nasara da aka ce a biya wadanda su ka shigar da kara N30bn a kan rusa masu hanyar neman abinci.
Daga baya Mai shari'a I. E. Ekwo ya bada umarnin a rufe asusun jihar Kano da ke CBN da sauran bankuna 24 saboda ganin an biya wadannan kudi.
3. Abba da Tsohon Gwamnan Kano
A shari’ar da aka yi a karkashin jagorancin A. Liman, kotun tarayya ta Kano ta haramtawa PCACA, ‘yan sanda, DSS da NSCDC cafke Abdullahi Ganduje.
Dr. Ganduje ya yi nasara wajen hana Hukumar PCACA taba shi, iyalinsa ko wadanda su ka yi aiki da gwamnatinsa na tsawon shekaru takwas a ofis.
4. Masu makarantu sun ja da Gwamnatin Kano
Bayan sauraron karar AbdulHafees D. Khalid, Alkali Nasiru Saminu na babban kotun Kano ya hana a dauki mataki a kan kungiyar masu makarantu.
‘Yan kasuwa masu makarantun kudi su sun yi galaba a gabar nan, babu damar a hana su kara kudin karatu bayan an dakatar masu da lasisi.
5. Mutanen gari da Abba a kotu
Kafin ayi wata daya da hawa mulki, wani Bakano mai suna Saminu Muhammad ya yi karar gwamnatin Kano, aka hana ta rusa shagunan mutane.
Lauyan Saminu Muhammad ya gamsar da Alkali S.A. Amobeda, aka umarci gwamnatin jihar ta dakatar da rusa shagunan jama’a a titin BUK.
6. Shari’ar kotun daukaka kara
Bayan rashin nasara a kotun sauraron karar zabe, da aka je kotun daukaka kara, lauyoyin APC ne su ka yi nasara a shari’ar zaben gwamnan Kano.
Alkalai uku sun tabbatar da hukuncin farko wanda ya zaftarewa NNPP kuri’u fiye da 165,000 sannan su ka ce Abba Kabir Yusuf ba ‘dan jam’iyya ba ne.
Abba Kabir Yusuf zai tsokano kotu
A dalilin rusau da aka yi a masallacin idi, ana da labari Alkalin kotun tarayya Samuel Amobeda ya ce Gwamnatin Abba za ta fitar da N30bn a mako guda.
Kotu ta gargadi Gwamnatin NNPP cewa sabawa hukunci da raina shari’a zai iya jawo dauri.
Asali: Legit.ng