Babbar Nasara: Luguden Wutar Sojojin Najeriya Ya Halaka Ƴan Ta'adda Sama da 160 a Jihohin Arewa 2

Babbar Nasara: Luguden Wutar Sojojin Najeriya Ya Halaka Ƴan Ta'adda Sama da 160 a Jihohin Arewa 2

  • Rundunar sojin saman Najeriya na Operation Hadin Kai ta halaka ƴan ta'adda sama da 160 a wani samame ranar 2 ga watan Nuwamba
  • An ce jirgin yaƙin NAF ya saki ruwan bama-bamai kan mafakar Boko Haram biyu a Yobe da Borno, sojoji ƙasa suka mara masa baya
  • Wannan na zuwa ne bayan Boko Haram ta kashe matasa 16 tare da dasa wa masu zuwa jana'iza Bam a ƙaramar hukumar Gaidam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

Rahotanni sun ce aƙalla mayaƙan kungiyar Boko Haram 160 ne suka bakunci lahira biyo bayan wani samame da jirgin yaƙin sojoji ya kai maboyarsu a jihohin Borno da Yobe.

Jirgin sojoji ya halaka tulin yan ta'adda.
Luguden Wutan Sojoji Ya Halaka Yan Ta'adda Sama da 160 a Jihohin Borno da Yobe Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Dakarun sojin saman Najeriya na rundunar Operation Haɗin Kai sun kaddamar da wannan ruwan wuta kan ƴan ta'addan ba kaƙƙautawa ranar Alhamis, 2 ga watan Nuwamba, 2023.

Kara karanta wannan

Sojoji zasu yi juyin mulki a Najeriya? Babban hafsan tsaro CDS Musa ya yi bayanin da ya kamata ku sani

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya tabbatar da haka a shafinsa na manhajar X watau Tuwita ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka ragargaji mayaƙan Boko Haram

Makama ya ce kjirgin sojin ya saki ruwan wuta a maɓoyar ƴan ta'addan guda biyu, na farko shi ne a Bulabulin da ke kan titin Ƙomadugu zuwa Kogin Yobe, kusa da ƙaramar hukumar Gaidam.

Wasu majiyoyi sun ce bayanan sirri sun nuna wannan sansanin ya tattara tulin ƴan ta'addan Boko Haram kuma daga nan suke ƙulla makircinsu kai hari kan fararen hula.

An ce daga nan mayaƙan suka shirya harin da suka kai ƙauyen Nguru Kayaya, ƙaramar hukumar Gaidam, inda suka kashe matasa 16, kana suka dasa Bam a lokacin da ake jana'iza.

A rahoton da ya tattara, Makama ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun yi fatali da tsagin Atiku, sun koma goyon bayan shugaba Tinubu kan abu 1 tak

"Daga nan jirgin yaƙi ya tunkari wurin ya saki ruwan wuta, wanda sojojin ƙasa suka mara masa baya, suka yi raga-raga da sansanin tare da kashe mayaƙan Boko Haram sama da 100."

Samame na biyu da sojojin suka kai sun kaddamar da shi ne a kauyen Degbawa da ke kusa da duwatsun Mandara a jihar Borno.

Yayin luguden wutan jirgin, ƴan ta'adda sama 60 suka baƙunci lahira ciki harda kwamandoji waɗanda aka ce suna tsaka da taron yadda za su kaiwa sojoji hari a Gwoza.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da CoS

A wani labarin kuma Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban ma'aikatan kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa, Usman Sahabi.

Rahotannin da aka tattara sun nuna cewa maharan sun kai masa farmaki har gida da daddare, suka tafi da shi zuwa cikin daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262