Ana Cigaba da Wahalar Samun Kudi da Wa'adin Canjin Tsofaffin N200, N500, Da N1,000 Ya Gabato

Ana Cigaba da Wahalar Samun Kudi da Wa'adin Canjin Tsofaffin N200, N500, Da N1,000 Ya Gabato

  • Mutane su na wahala wajen samun kudi a sakamakon gabatowar lokacin da aka yanke na daina amfani da tsofaffin Nairori
  • Muddin wa’adin da aka yanke bai canza ba, daga shekarar nan ba za a sake aiki da tsofaffin takarun N200, N500 da N1000 ba
  • Tun kafin lokacin ya yi, kudi sun fara yankewa a bankuna da hannun mutane, hakan ya nuna babu isassun sababbin takardu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Nan da 31 ga watan Disamba za a daina amfani da tsofaffin N200, N500 da N1000 kamar yadda kotun koli ta zartar da hukunci.

A halin da ake ciki, binciken Daily Trust ya nuna an koma gidan jiya wajen wahalar samun kudi a garuruwan Kano, Borno da sauransu.

Kara karanta wannan

Tinubu zai kashe Naira Biliyan 1.5 wajen sayo motocin uwargidar Shugaban kasa

‘Yan kasuwan Kano da Borno sun ce su na fuskantar karancin takardun Nairori a sakamakon canjin da bankin CBN ya yi a shekarar nan.

Naira
Ana shan wahalar samun Naira Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu POS sun ce babu kudi a gari

Rahoton ya ce masu harkar POS su na kukan cewa ba su da kudin da za su iya ba mutum sama da N20, 000 domin babu kudi a bankuna.

Idan mutum ya je cire kudi a banki, N40, 000-N50, 000 kadai ake iya karba a rana, kamfanoni kuma su na samun N150, 000 – N200, 000.

"Babu kudin a nan" - Ma'aikacin banki

Legit ta zanta da wani ma’aikacin banki da ke aiki a jihar Kaduna, ya tabbatar mana da cewa haka abin yake, bai bari mun kama sunansa ba.

"Ko mu yanzu idan ka zo banki ba za ka samu N50, 000, ana wahalar kudi.

Kara karanta wannan

Naira ta farfado sosai a kasuwar canji, watakila Dala ta karye kwanan nan

Kuma tsofaffin ne ake daukowa ana biyan mutane da su, musamman takardun N200, babu sababbin kudin sosai."

- Ma'aikacin banki

Wani mai kasuwancin POS a karamar hukumar Giwa ya bayyana mana sun kara yawan kudin da su ke karba saboda halin da ake ciki.

An koma shaguna, babu kudi a ATM

Da mu ka bincika na’urorin ATM a bankunan da ke garin Zariya, mun fahimci babu kudi sosai, an fi samun kudi a shaguna da kasuwanni.

Mutane su kan samu kudi a gidajen mai wanda su ma kasuwancinsu ya ragu sosai musamman bayan cire tallafin man fetur a watan Mayu.

Shawarar yadda Naira za ta mike

Ana da rahoto cewa Cif Olusegun Obasanjo ya fadawa gwamnati a guji kayan kasar Sin idan ana so Naira ta mike ganin darajarta ta karye.

Tsohon Shugaban Kasar ya ce halatta bada Dala da bankin CBN ya yi domin a rika shigo da kayan kasar waje zai kashe ‘yan kasuwan gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel