Daga Nada Shi, Shugaban Hukumar Tsaro Ya Ajiye Aiki Kan Zargin 'Alaka' da ‘Yan Bindiga

Daga Nada Shi, Shugaban Hukumar Tsaro Ya Ajiye Aiki Kan Zargin 'Alaka' da ‘Yan Bindiga

  • Garba Moyi Isa ya hakura da kujerar da aka ba shi na shugaban kwamitin kafa jami’an tsaron sa-kai a Sokoto
  • Tsohon sojan ya nuna ba zai saida mutunci da kimarsa saboda mukami ba, ya yi watsi da kujerar da ya samu
  • Kanal Garba Moyi (rtd) ya yi murabus a karshen makon jiya ba tare da ya fadi abin da ya jawo ya ajiye aikin ba

Sokoto - Jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kwamitin da zai kafa jami’an tsaron sa kai, Garba Moyi Isa ya yi murabus.

Rahoto ya zo daga Leadership cewa Kanal Garba Moyi Isa mai ritaya ya sauka daga kujerar da gwamnatin jihar Sokoto ta nemi daura shi.

Garba Moyi Isa ya yi murabus ne bayan ‘yan awanni da rantsar da kwamitinsa mai mutum 25 a yunkurin an kawo zaman lafiya a Sokoto.

Kara karanta wannan

Hakikanin Abin da Ya Faru – Gwamna Ya Yi Bidiyon Karyata 'Harin' da Aka Kai Masa

Yan Bindiga
Sojoji su na yaki da 'yan bindiga a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Garba Moyi Isa da 'yan bindiga a Sokoto

Ana tunani tsohon sojan ya dauki wannan mataki ne saboda wani bidiyo da aka fitar, ana zargin ya na da alaka da ‘yan ta’addan da ke Sokoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Garba Moyi wanda ya rike kujerar Kwamishina har sau uku a jihar Sokoto, ya tara manema labarai a karshen makon jiya, ya yi jawabi.

Tsohon jami’in tsaron ya yi bayanin yadda ya bautawa kasarsa na shekara da shekaru a gidan soja, daga baya kuma ya shigo siyasa.

Ko a rahoton da aka samu daga jaridar Punch, haka dai aka ji cewa Moyi bai bada asalin abin da ya jawo ya ajiye kujerar da aka ba shi ba.

Jawabin murabus shugaban kwamitin tsaro

"Na bautawa kasar nan har sa da na yi ritaya a matsayin Kanal, bayan nan sai na shiga siyasa, na zama shugaban karamar hukuma ta.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Tsageru sun yi yunkurin kashe gwamnan APC a Arewa, bayanai sun fito

Sannan na yi Kwamishina na tsaro a lokuta uku har na ajiye aiki a gwamnatin da ta wuce ba tare da wata matsala ba.
Ba zan taba saida mutunci na da komai ba. Babu mukamin da ya kai daraja ta, saboda haka na ajiye kujera ta.
Na godewa Mai girma Gwamna Ahmed Aliyu da ya ga na cancanta ya ba ni mukamin nan.
Ina mai tabbatarwa Mai girma Gwamna da daukacin mutanen jihar cewa aikinsu na ke yi, kuma zan cigaba da bada gudumuwata wajen cigaban jihar.

- Garba Moyi Isa

An kai wa Gwamna Bello hari?

A jiya ne kuma aka samu labari Gwamnan Kogi ya tabbatar da cewa miyagu ba su kai wa tawagarsa wani hari a hanyar zuwa Abuja ba.

Gwamna Yahaya Bello ya karyata Kwamishinansa, ya ce sabani aka samu kurum da sojoji, zuwa yanzu gari ya dauki zafi a shirin zaben Kogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng