Kwamishinan Tsaro na Gwamna Tambuwal ya Koma APC a Sokoto

Kwamishinan Tsaro na Gwamna Tambuwal ya Koma APC a Sokoto

  • Jam'iyyar PDP na ci gaba da ganin tasku a Sokoto yayin da na hannun daman gwamna ya sauya sheka
  • Jam'iyyun APC da PDP na ci gaba da kwace mambobi daga rumfunan juna gabanin babban zaben 2023
  • A makon nan ne baya ga jihar Sokoto, a Kebbi aka samu yawaitar sauya sheka tsakanin APC da PDP

Jihar Sokoto - Al'amuran siyasa a jihar Sokoto na kara canzawa gabanin babban zaben badi. Jam’iyyar PDP mai mulkin jihar ta rasa wasu ‘ya’yanta zuwa jam’iyya mai mulkin kasa; APC.

Kanar Garba Moyi (rtd), wanda shi ne kwamishinan ayyuka da harkokin tsaro a gwamnatin Gwamna Aminu Tambuwal ya fice daga PDP ya tsunduma APC, The Nation ta ruwaito.

Ficewar Moyi na zuwa ne jim kadan bayan jam’iyyar ta karbi Kalanjeni da kansilolinsa wadanda su ma suka fice daga PDP zuwa APC a karkashin Sanata Aliyu Wamakko a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

APC Ta Faɗi Sunan Wani Gwamnan PDP Dake da Hannu a Matsalar Tsaron Jiharsa, Ta Nemi a Kayar da Shi a 2023

Kwamishinan Tambuwal ya shiga APC, ya bar PDP
Bikin sauya sheka: Kwamishina Tambuwal ya koma APC a Sokoto | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wata sanarwa da mataimaki na musamman kan sabbin kafafen yada labarai na Sanata Wamakko, Bashir Abubakar ne ya fitar da rahoton shigowar Moyi APC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, Moyi ya fice daga tsohuwar jam’iyyarsa ne saboda rashin amana da mayar da hankali da shugabanci na gari. Moyi ya ce gwamnatin Tambuwal ta karyata alkawarin da ta yi wa al’ummar jihar Sokoto.

Moyi ya ce:

“Na lura da farin ciki ga mutuntaka, tushe da ingantaccen jagoranci na Sanata Wamakko. Wannan ne ya kara min kwarin gwiwa na ficewa daga jam’iyyar PDP, don haka zan iya kasancewa cikin tarihinsa da ba a taba ganin irinsa ba.
“Abin alfahari ne a samu wani irin Sarkin Yamman Sokoto, kuma ya kamata mutane irina su ba su goyon baya domin a samu nasarar gudanar da al’amuran jam’iyyar APC na Sokoto."

Sanata Wamakko wanda ya tarbi Moyi a gidansa ya bukace shi, kamar sauran mutane, da ya yi aiki tukuru domin kawo nasara ga jam’iyyar, musamman a yankin Sanatan Sokoto ta Gabas da ma jihar baki daya a zaben badi, haka nan Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Jam'iyyar PDP ta dage zaman NEC saboda ta'azzarar rikicin gida

Wadanda suka halarci liyafar karbar sun hada da dan takarar gwamnan Sokoto, Idris Muhammad Gobir.

Hakazalika da Dan takarar Sanatan Sokoto ta Gabas, Ibrahim Lamido Isa; da takwaransa na majalisar wakilai, Abdulkadir Jelani Danbuga; da kuma shugaban karamar hukumar Sabon Birni, Alhaji Yawale Sarkin Baki.

Dan Majalisar Wakilai Yakubu Rilisco Ya Fice Daga PDP Ya Dawo APC a Kebbi

A wani labarin, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Birnin Kebbi, Kalgo da Bunza, Hon Bello Yakubu Rilisco ya ficewarsa daga PDP ya koma ta APC, rahoton TVC.

Dan majalisar na tarayya ya shaidawa manema labarai a Birnin Kebbi a ranar Litinin cewa ya yanke sauya sheka ne saboda muradinsa na hada karfi da karfe da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu domin kai jihar ga wani matsayi mai girma.

Relisco dai ya koma PDP ne domin ya tsaya takara a zaben fidda gwani na kujerar da yake kai a halin yanzu, inda ya sha kaye a hannun Barista Bello Halidu, dan tsohon shugaban PDP na kasa.

Kara karanta wannan

Dan majalisan da ya gudu a APC saboda neman kujerar takara a PDP ya dawo, ya rasa tikiti

Asali: Legit.ng

Online view pixel