Wani jirgin Sojin saman Najeriya yayi hadari wajen fama da Boko Haram
- Jirgin yakin Sojojin Najeriya ya fadi wajen yakar ‘Yan Boko Haram
- Shugaban Hafsun Sojojin sama yace za ayi bincike game da lamarin
- An yi dace babu wanda ya rasu a wajen wannan hadari da ya auku
Mun ji cewa Rundunar Sojin Najeriya ta gamu da babban asara a yakin da ta ke yi da ‘Yan ta’addan Boko Haram a cikin Kasar. Wani jirgin saman Sojojin Najeriyar ne ya fadi yayin da ake fada da ‘Yan ta’addan.
Rundunar Sojojin sama na Najeriya ta tabbatar da aukuwar wannan mummun abu. Jami’in da ke kula da yaa labarai na Rundunar watau Air Vice Marshal Olatokunbo Adesanya ya bayyana wannan kamar yadda labari ya zo mana yanzu nan.
KU KARANTA: An kama wasu kwayoyi da za a shigo da su Najeriya
Wani jirgin sama na Sojojin saman Najeriya na MI-17 ne yayi hadari wajen fama da Boko Haram da ke Yankin Arewa maso yammacin Kasar nan. Hadarin ya faru ne a yau Litinin dinnan amma an dace babu wanda ya rasa ran sa a sanadiyyar hakan.
Air Marshal Sadique Abubakar wanda shine Shugaban Hafsun Sojin sama na Kasar yace za ayi bincike wajen ganin abin da ya sa jirgin ya fadi. Sojojin dai na kokarin ganin bayan ragowar ‘Yan Boko Haram da ke Yankin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng