OPC, Dakarun Amotekun da Wasu Kungiyoyi Sun Yi Artabu da Makiyaya a Oyo

OPC, Dakarun Amotekun da Wasu Kungiyoyi Sun Yi Artabu da Makiyaya a Oyo

  • Jami'an tsaron Amotekun, OPC, da wasu ƙarin biyu sun yi gumurzu da Fulani makiyaya a jihar Oyo
  • Rahoto ya nuna Makiyaya nw suka tsokano faɗan kuma suka yi wa jami'an kwantan bauna, ana fargabar da yawa sun mutu
  • Har yanzun ba bu wani cikakken bayani daga hukumar 'yan sandan reshen jihar Oyo kan wannan sabon lamari da ya auku

Jihar Oyo - Rahotanni sun nuna cewa jama'a sun shiga tashin hankali a ƙauyen Iwerele da ke ƙaramar hukumar Iwajowa a jihar Oyo yayin da ake fargabar an rasa rayuka da dama.

Punch ta ce ana tsammanin mutane da yawa sun mutu a wani aratabu da aka yi tsakanin dakarun Odudua, jami'an tsaron rundunar Amotekun, jami'an Operation Burst, Soludero da fulani makiyaya.

Jami'an tsaro sun fafata da Fulani makiyaya.
Jami'an haɗin guiwa sun yi gumurzu da mayaƙan Fulani makiyaya Hoto: punch
Asali: Twitter

Har yanzun dai ba a san ainihin maƙasudin abin da ya tada wannna rigima ba, amma jaridar ta samu bayanai daga majiya mai tushe a yankin.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Shiga Ƙaramar Hukuma 1 a Jihar Kano, Sun Kashe Mutane Sun Sace Wasu da Yawa

Asalin abin da ya tada rikicin

Majiyar ta bayyana cewa wasu makiyaya ne suka kutsa kai cikin gona a yankin garin, kuma suka kiwata shanunsu a ciki, lamarin da ya kai ga kashe mai gonar yayin musayar yawu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wakilin jaridar ya tattaro cewa nan take aka umarci jami'an tsaron haɗin guiwa da suka ƙunshi, Operation Burst, OPC, Amotekun da Soludero su tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Makiyaya sun yi wa jami'an tsaro kwantan ɓauna

A kan haryarsu ta zuwa yankin domin dawo da kwanciyar hankali ne kwatsam sai Fulani makiyaya suka ɗana musu tarko, suka musu kwantan ɓauna.

Wannan lamari ya yi ajalin mutane da yawa wanda har yanzun ba a gama tantance adadin yawansu ba.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, duk wani kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso bai kai ga nasara ba.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jami'an Tsaro Sun Mamaye Babbar Sakateriyar Jam'iyyar PDP Ta Jiha, Bayanai Sun Fito

Bai ɗaga kiran wayar da aka masa ba kuma bai turo amsar saƙonnin kar ta kwana da aka tura masa kan wannan lamarin ba.

Yan Bindiga Sun Sace Mutane da Yawa a Ƙaramar Hukumar Jihar Kano

A wani rahoton na daban kuma 'Yan bindiga sun kashe mutane sun yi garkuwa da wasu da ba a tantance yawansu ba a karamar hukumar Ƙaraye ta jihar Kano.

Mazauna ƙauyuna Yola da abun ya faru sun ce maharan sun kai hari a jere, sun tafka ta'asa tun daga ranar Asabar da ta wuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel