Auren Gata a Kano: Hotunan Gadaje, Kayan Abinci, Da Kayayyakin Da Gwamnati Ta Rabawa Ma’aurata

Auren Gata a Kano: Hotunan Gadaje, Kayan Abinci, Da Kayayyakin Da Gwamnati Ta Rabawa Ma’aurata

  • An sha shagalin bukukuwa a Kano yayin da gwamnatin jihar ta yi wa mata 1800 auren gata
  • An bai wa amaren wadanda yawancinsu zawarawa ne kudin sadaki N50,000 a madadin kowani ango, sannan an yi masu kayan daki, gara da tufafi
  • An zabo ma'auratan wadanda suka kasance zawarawa, wadanda mazajensu suka mutu da yan mata daga fadin kananan hukumomi 44 na jihar

Jihar Kano - A makon jiya ne gwamnatin jihar Kano ta yi gagarumin biki inda ta yi wa ma'aurata 1800 auren gata.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf wato Abba Gida-Gida ya dauki nauyin auren gaba daya.

A yayin daurin auren da aka yi a masallacin fadar sarkin Kano, Kwankwaso ne ya tsaya a matsayin wakilin angwanai 1,800 yayin da Gwamna Yusuf ya wakilci amaren.

Kara karanta wannan

Kano: An Kama Mutum 30 Kan Yunkurin 'Tayar da Tarzoma' a Wurin Auren Gata 1,800, Sun Yi Bayani

Gwamnatin Kano ta yi wa sabbin ma'auratan kayan daki
Auren Gata a Kano: Hotunan Gadaje, Kayan Abinci, Da Kayayyakin Da Gwamnati Ta Rabawa Ma’aurata Hoto: Sodiq Adelakun
Asali: Twitter

Gwamnatin Kano ta biya N50,000 a madadin kowani ango

Channels TV ta rahoto cewa yawancin wadanda suka ci gajiyar wannan aure nna gata sun kasance zawarawa da wadanda mazajensu suka mutu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da kari, gwamnatin jihar ta biya kudin sadaki N50,000 ga kowace amarya a madadin angwanen.

An bai wa sabbin ma'auratan Kano gadaje, kayan gara da tufafi

Daga cikin tanadin da aka yi wa masu auren gatan, gwamnati ta bai wa ma'auratan gadaje, zaunnuwan gado, kayan abinci da kuma tufafin sanyawa, rahoton Vanguard.

An kuma tattaro cewa ma'auratan za su biya gwamnatin jihar kayayyakinta idan suka rabu.

A martaninsa, Gwamna Yusuf ya bayyana taron a matsayin shaida na jajircewar jihar wajen inganta al'adu da zamantakewa tsakanin al'umma.

Auren gata: Kwankwaso ya fadawa ma’aurata sirrin yadda za su zauna lafiya

Kara karanta wannan

Gwammatin Tinubu Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Mutane Aikin N-Power Na 2023? Gaskiya Ta Bayyana

A gefe guda, Rabiu Musa Kwankwaso wanda jagora ne a jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano ya halarci walimar auren gata da aka shirya.

Gwamnatin jihar Kano ta aurar da maza da mata 1, 800, Daily Trust ta rahoto abin da ya wakana wajen walimar auren da aka yi a yau.

An gudanar da walimar ne a gidan gwamnati, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa ma’uratan hudubar yadda za su zauna lafiya.

Tsohon gwamnan ya ja-kunnensu a game da duba wayoyin mazajensu, yake cewa laluben salulan ya na yawan kashe aure a yau. Kwankwaso ya bada shawara ga sababbin auren su guji abin da zai iya kawo matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng