Ana Babu Kudi, An Kammala Shirin Rabawa ‘Yan Majalisa Motocin Naira Biliyan 40

Ana Babu Kudi, An Kammala Shirin Rabawa ‘Yan Majalisa Motocin Naira Biliyan 40

  • Majalisar wakilan tarayya ta tabbatar da za ta rabawa ‘ya ‘yanta manyan motoci wadanda ake kukan za su ci biliyoyin kudi
  • Jawabin Hon. Akin Rotimi ya tabbatar da hakan, sai dai an fahimci za a ba ‘yan majalisa motocin ne domin su ji dadin aiki
  • Sanatoci da ‘yan majalisar tarayya sun saba hawa manyan motoci, ‘dan majalisar ya ce ba a kan su aka kawo al’adar nan ba

Abuja - A daidai lokacin da mafi yawan al’umma su ke neman kudin abinci, majalisar wakilan tarayya ta ke shirin rabawa kan ta motoci.

An samu rahoto daga Daily Trust cewa an fitar da jawabi da ya nuna ‘yan majalisar tarayya za su samu sababbin motoci domin yin aiki.

Shugaban kwamitin yada labarai da hulda da jama’a na majalisar, Akin Rotimi ya saki jawabi domin ya yi karin haske a kan lamarin.

Kara karanta wannan

"Na Shirya Sadaukar da Rayuwata Domin Kawo Karshen Yan Bindiga" Gwamnan Arewa

Motocin 'Yan majalisa
Irin motocin da za a rabawa 'Yan majalisa Hoto: @ReporteraNews
Asali: Twitter

Majalisa ta ce ana zuzuta batun motoci

Hon. Akin Rotimi ya ce hakan ya zama dole a lokacin da rahotanni iri-iri su ke yawo, sai su ka ga bukatar sanar da gaskiyar halin da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan majalisar yake cewa ana zuzuta labarin, sai dai ya tabbatar da gaskiyar maganar, amma bai fadi farashin da za a saye motocin ba.

Honarabul Rotimi ya ce akwai matakai da ake bi wajen shigowa da rabawa ‘yan majalisa motoci, ya kara da cewa haka aka saba a majalisa.

"Ba mu aka fara ba mota ba" - Majalisa

"Ba a majalisa kadai ake yin wannan ba, jami’an gwamnatin da ba zababbu ba a bangaren zartarwa, tun daga Mataimakan Darektoci zuwa sama, a mafi yawancin lokaci su na da motocin ofis."

- Hon. Akin Rotimi

Mai magana da yawun ‘yan majalisar ya kara da cewa motocin da za a raba masu na aikin ofis ne, don haka ba kyauta aka mallaka masu ba.

Kara karanta wannan

Gaza: Saudiyya Ta Kira Taron Musulmai, Fafaroma Ya Tsawata Wa Isra'ila

Aron mota za a ba 'yan majalisa ko kyauta?

Kamar yadda Leadership ta kawo, idan ‘dan majalisa zai bar matsayin da ya ke kai a 2027, motar za ta bar hannunsa sai dai idan an saida masa.

Ana kukan motocin sun yi tsada, majalisa ta ce amfanin manyan motoci shi ne ratsa ko ina saboda yadda ake fama da rashin kyawun hanyoyi.

Zai yi kyau ‘dan majalisa ya iya shiga ko ina domin bada wakilci da kyau, saboda haka Akin Rotimi ya ce ake kashe kudi a kan abin hawa.

Motocin 'yan majalisa zai ci kusan N50bn

Kwanakin baya rahoto ya zo cewa kwamitin da yake kula da harkokin majalisar za a ba dawainiyar shigo da manyan motocin zuwa aiki.

‘Yan majalisar wakilan tarayya da Sanatoci da ke ofis za samu sababbin motocin Toyota Landcruiser da Prado na kusan Naira biliyan 50.

Asali: Legit.ng

Online view pixel