Sanatoci, ‘Yan Majalisa Za Su Kashe Naira Biliyan 40 a kan Motoci Masu Numfashi

Sanatoci, ‘Yan Majalisa Za Su Kashe Naira Biliyan 40 a kan Motoci Masu Numfashi

  • Sama da N40bn za a batar a Majalisar wakilan tarayya da Majalisar dattawa domin tanadin motoci
  • Yemi Adaramodu ya ce ‘Yan majalisa za su biya kudin motocin daga cikin albashinsu da alawus
  • Majalisar tarayya ta karyata batun cewa N70bn da aka ware masu za su tafi ne wajen sayen motoci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Ba da dadewa ba, Majalisar wakilan tarayya da Majalisar dattawa za ta kashe fiye da Naira Biliyan 40 wajen sayen motoci ga ‘ya ’yanta.

Sun ta samu labarin cewa ‘yan majalisar tarayya za su saye manyan motoci na zamani da ake yay bayan rantsar da su a ofis a watan jiya.

A halin yanzu ana shirin sayo motocin Toyota Landcruiser ta 2023 akalla 107 ga Sanatoci.

Sanatoci
Sanatoci za su samu Landcruiser 2023 a Majalisa Hoto: Nigerian Senate Hoto: sellatease.com
Asali: UGC

Ba a bar 'Yan majalisa a baya ba

Kara karanta wannan

Hadimar Tinubu Ta Ayyana Bangaren da Gwamnatin APC Za Ta Maida Hankali a Kai

Sannan kuma za a sayowa ‘yan majalisar wakilan tarayya motar Toyota Prado ta shekarar 2023, rahoton ya ce za a kawo masu motoci har 358.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan lissafin bai hada da motocin da za a sayowa shugabannin majalisar kasar; Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas da mataimakansu ba.

Sanata Jibrin Barau da Benjamin Kalu za su samu sababbin motoci da ke tashe yau a Duniya.

Irin motocin da za a nemo

Jaridar ta ce za a nemo motoci masu dadin tafiya wadanda ke da kyamara da irinsu Apple CarPlay, Android Auto da babban sifika saboda jin sauti.

Wadannan motoci masu kujeru goma su na da kujeru masu daukar sanyi da zafi a lokacin da ya dace, kuma ana iya cin caji ba tare da waya ba.

Wani dillalin mota ya shaida cewa ana bukatar fiye da N300m domin sayen kowace daga cikin wannan mota saboda karyewar Naira a kasuwa.

Kara karanta wannan

Ja Ya Faɗo-Ja Ya Ɗauka: ‘Yan Majalisar Tarayya Sun Amince a Kashe Masu N70bn

Wannan karo ‘yan majalisar wakilai za su yi amfani da Prado jeeps a maimakon Toyota Camry 2019 da aka rabawa ‘yan majalisa ta tara a 2019.

Za a saye motocin N70bn?

Mai magana da yawun majalisar dattawa, Sanata Yemi Adaramodu ya ce sannu a hankali abokan aikinsa za su biya duk kudin da aka kashe masu.

Adaramodu ya ce maganar sayen motocin N70bn ba gaskiya ba ne, ya kare majalisar da cewasu na bukatar motoci domin su iya yin aiki da kyau.

'Yan majalisa sun samu karin kudi

Rahoton nan ya nuna a karin Naira biliyan 819 da gwamnatin tarayya za ta kashe a kasafin kudin shekarar nan, 'yan majalisa su na da kimanin 8.5%.

Ana sa ran wadannan kudi su taimakawa ‘yan siyasar wajen aiki da kyau. Za a batar da N70bn domin yi wa sababbin shiga maraba da zuwa majalisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel