Jerin Jihohin Da Suka Samu Sakamako Mai Kyau Da Akasin Haka a NECO 2023

Jerin Jihohin Da Suka Samu Sakamako Mai Kyau Da Akasin Haka a NECO 2023

Minna, jihar Neja - Hukumar shirya jarabawa ta ƙasa (NECO) a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba, ta fitar da sakamakon jarabawar manyan makarantun sakandare (SSCE) na shekarar 2023.

A wata zantawa da manema labarai, shugaban hukumar NECO, Farfesa Dantani Wushishi, ya ce sakamakon ya nuna cewa kaso 61.6% cikin 100 ne suka samu kiredit biyar da suka haɗa da Lissafi da Ingilishi, cewar rahoton The Nation.

Sakamakon NECO 2023 ya fito
An fitar da sakamakon NECO 2023 Hoto: NECO, Deeper Life High School
Asali: Facebook

A yayin da yake bayyana fitar da sakamakon jarabawar SSCE na 2023, Farfesa Wushishi ya kuma bayyana cewa jihar Abia ce ta fi yawan ɗalibai da suka samu kiredit biyar ko sama da haka da suka hada da lissafi da Ingilishi da kaso 85.53%.

Adamawa ce ta zo ta biyu da kaso 51.5%, yayin da jihar Kebbi ke da kaso mafi ƙaranci inda ta samu kaso 0.310%.

Kara karanta wannan

Malamin Makaranta Ya Ɗebo Ruwan Dafa Kansa Bayan Ya Zane Ɗaliba Mace a Abuja

A cikin wannan rahoton, Legit.ng ta yi nazari kan jihohin da suka yi fice da waɗanda aka bari a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1) Jihar Abia (wacce ta zo ta ɗaya)

Abia jiha ce da ke a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya. Ita ce jiha ta 32 mafi girma a Najeriy kuma ta 27 mafi yawan jama'a inda take da yawan jama'a sama da 3,727,347 a zuwa shekarar 2016.

Tun farko a shekarar 2023, gwamnatin jihar Abia ta ayyana cewa ba za ta amince da makarantun da ba su da inganci ba.

Wataƙila hakan ya ba da gudunmawa ga kyakkyawan sakamakon da ɗaliban makarantun sakandare na jihar Abia suka samu a jarabawar NECO ta 2023.

2) Jihar Adamawa state (ta biyu wacce ɗalibanta suka yi ƙoƙari)

Jihar Adamawa jiha ce da ke a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hukumar NECO Ta Saki Sakamakon Jarabawar Bana SSCE 2023

Akwai makarantun sakandare da firamare da yawa da kwalejojin fasaha da makarantu masu zaman kansu a Adamawa.

Haka kuma jihar tana da makarantar koyon aikin jinya da unguwar zoma, da makarantun koyar da sana'o'i guda biyu, da kwalejin nazarin shari’a a babban birnin jihar.

Jihar da ke da ɗaliban da ba su samu sakamako mai kyau ba

Jihar Kebbi

Jihar Kebbi na yankin Arewa maso Yamma na Najeriya. Jihar Kebbi an samar da ita ne daga cikin jihar Sokoto a ranar 27 ga watan Agustan 1991.

Daga cikin jihohi 36 na Najeriya, Kebbi ita ce ta goma mafi girma kuma ta 22 mafi yawan jama'a, inda aka ƙiyasta yawan jama'a kusan miliyan 4.4 a shekarar 2016.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin jihar Kebbi na daukar ilimi a matsayin babban abun kawo cigaba.

NECO Ta Saki Sakamakon Jarabawar 2023

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar shirya jarabawa ta ƙasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala karatun manyan makarantun sakandare (SSCE) na bana.

Hukumar ta kuma kama wasu makarantu da laifin yin satar amsa, inda ta ce za ta ɗauki mataki a kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel