Kotu ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan matashin da ya kashe mahaifinsa

Kotu ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan matashin da ya kashe mahaifinsa

Wata kotu ta musamman da ke zamanta a Ikeja ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani bakanike, Rasak Abiona, wanda ya kashe mahaifinsa mai shekaru 62 ta hanyar bugunsa da karfen rodi a ka.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa alkalin kotun, Jastis Oluwatoyin Taiwo, ta zartar da hukuncin ne yayin zaman kotun da aka yi ranar Litinin ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Rasak ya kashe mahaifinsa ne sakamakon sabanin da su ka samu a kan wata kadara da ke Legas.

Jastis Taiwo ta ce ma su kara sun gabatar da isassun shaidun da su ka kore duk wani shakku tare da tabbatar da cewa matashin ne ya kashe mahaifinsa.

Alkaliyar ta ce wanda ake zargi ya amsa laifinsa a cikin rahoton da ya rubuta a ofishin rundunar 'yan sanda.

Kazalika, ta bayyana cewa ya gaza kare kansa ko gabatar da wata kwakwarar hujja da za ta wanke shi daga zargin da ake yi ma sa.

Kotun ta ce wanda aka gurfanar ya gaza gabatar da hujjar da za ta gamsar da kotu cewa mahaifinsa ya mutu ne sakamakon faduwar da ya yi a kan karfen rodi.

Kotu ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan matashin da kashe mahaifinsa
Kotu ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan matashin da kashe mahaifinsa
Asali: UGC

Jastis Taiwo ta yankewa Rasak hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin aikata kisan kai, laifin da ya sabawa sashe na 221 na kundin manyan laifuka a jihar Legas, wanda aka kirkira a shekarar 2011.

"Wannan ba kankanin abin bakin ciki ba ne a ce da ya kashe mahaifinsa.

"Babu shakka ya yi niyyar kashe mahaifinsa, ba don hakan ba, ba zai buga ma sa karfen rodi a kansa ba.

DUBA WANNAN: Salon nadin mukamanka zai tarwatsa Najeriya - Kanal Dangiwa Umar ya rubutawa Buhari wasika

"Matashin ya fi karfin dattijon mahaifinsa mai shekaru 62, zai iya cin galaba a kansa ba tare da ya yi amfani da karfi ya huda ma sa kai ba.

"Wannan shine laifi ma fi muni da rashin hakuri da zuciya za su iya tunzura mutum ya aikata a rayuwarsa.

"Kotu ba ta da wani uzuri na yanke hukunci mai sassauci a kan laifin kisa, musamman idan aka yi la'akari da sashe na 223 na kundin hukuncin manyan laifuka na shekarar 2011.

"Na yankewa wanda ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe mahaifinsa, Sunday Abiona. Wannan hukunci ne da kotu ta zartar," a cewar alkaliyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel