Satifiket Din Da Tinubu Ya Bai Wa INEC Ba Jabu Bane, In Ji Jami’ar Jihar Chicago

Satifiket Din Da Tinubu Ya Bai Wa INEC Ba Jabu Bane, In Ji Jami’ar Jihar Chicago

  • Jami'ar CSU ta tabbatar da ingancin takardar shaidar karatu da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatarwa hukumar INEC a zaben 2023
  • Jami'ar ta jihar Chicago ta ce takardar da aka bai wa Tinubu lokacin da ya kammala karatu a 1979 da wanda ya gabatarwa INEC duk suna da inganci
  • CSU ta ce an samu bambance-bambance a takardun ne saboda jami'ar ta sabonta hatiminta bayan bayar da satifiket din

Jami'ar jihar Chicago ta tabbatar da ingancin takardar shaidar karatu da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya gabatarwa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a lokacin zaben shugaban kasa na 2023.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Jami'ar jihar Chicago ta tabbatar da cewar satifiket din da wanda aka ba shugaban kasa Tinubu a lokacin da ya kammala karatu a 1979 suna da inganci.

Kara karanta wannan

Lamari Ya Canza da Jami’ar Amurka Ta Yi Karin Haske Dangane da Takardar Tinubu

Jami'ar Chicago ta tabbatar da ingancin satifiket din Tinubu
Satifiket Din Da Tinubu Ya Bai Wa INEC Ba Jabu Bane, In Ji Jami’ar Jihar Chicago Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Within Nigeria ta rahoto cewa a cikin takardar da ta gabatarwa kotun a Chicago, jami'ar CSU ta ce:

"Jami'ar jihar Chicago ta ba Bola Ahmed Tinubu takardar Difloma sannan daga baya ta ba da kwafin satifiket din wannan Difloma. Dukkansu suna da inganci kuma sahihin satifiket din jami'ar jihar Chicago ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Akwai yan bambance-bambance tsakanin Diflomar da satifiket din saboda shugaba mai ci/shugaban hukuma na yanzu ne ke sa hannu a dukkanin takardun diflomar. Haka kuma akwai bambance-bambance a girman rubutu da hatimin da ke kan Diflomar saboda jami'ar ta sabonta hatiminta bayan bayar da takardar.
"Bambanci da aka samu a ranar da aka ba da takardar diflomar da na satifiket din na iya kasancewa kuskuren dan adam wanda yake ajizi. Mutum ne ke buga kwanan wata da ke rubuce kan satifiket da hannu kuma yana iya zuwa da kuskure."

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Zama Shugaban Najeriya Na Farko Da Kotun Koli Za Ta Tsige – Hadimin Atiku

Ba mu da takardar shaidar da Tinubu ya mikawa INEC – Jami’a

Hakan na zuwa ne bayan jami’ar CSU da ke kasar Amurka ta ce ba ta dauke da irin takardar shaidar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatarwa INEC.

Caleb Westberg wanda shi ne Magatakardar jami’ar ya shaida haka da yake amsa tambayoyi, Daily Trust ta fitar da rahoton a ranar Laraba.

Kamar yadda Lauyoyin Atiku Abubakar su ka bukata a kotu, an kira jami’in jami’ar ya amsa wasu tambayoyi da za su taimakawa binciken.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng