Mutumin Da Ya Sauya Siffarsa Zuwa Ta Kare Ya Koka, Ya Ce Karnukan Gaske Sun Ki Wasa Da Shi

Mutumin Da Ya Sauya Siffarsa Zuwa Ta Kare Ya Koka, Ya Ce Karnukan Gaske Sun Ki Wasa Da Shi

  • Wani mutum mai suna Toco ya sauya siffarsa zuwa ta kare ta hanyar amfani da wata sutura mai nuna jiki sak na kare tsabar tsananin son ya zama dabba
  • Duk da kashe makudan kudade wurin yin wannan sauyi, Toco ya bayyana rashin jin dadinsa ga yadda karnuka ke nuna masa wariya
  • A yanzu haka dai ana ambatonsa a matsayin mutumin da ke ji a ransa shi ba dan adam bane, ya fi karkata tunani da hangensa a matsayin kare

Wani mutumin da ya kashe kudadensa wurin sauya kamanninsa zuwa na kare ya bayyana bacin rai da rashin jin dadinsa yayin da karnukan gaske suka ki wasa dashi.

Pooch-wannabe Toco ya shahara a kwanakin bayan nan bayan ya yada wani faifan bidiyonsa sanye da wata tufa mai siffar kare yana tafiya a birnin Tokyo ta Japan.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Nunawa Duniya Karamar Yarinyar Da Ya Tsinta a Bola, Ta Zama Kyakkyawa Shar Da Ita

Mutumin da ya so sauyawa zuwa kare na bayyana kukansa
Ya maida kansa kare, amma karnuka ba sa wasa dashi | Hoto: @I_want_to_be_an_animal.
Asali: UGC

Me yasa Toco ya ji takaici kan yadda sauyinsa bai ga ruwa ba?

Duk da manyan kudaden da ya zuwa wajen wannan aikin na maida kansa dabba, kokarin bai kai ga nasara ba, domin karnukan gaske ba sa mu'amalantarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata tattaunawa da jaridar The Sun, Toco ya bayyana rashin jin dadinsa da takaici, inda yace:

"Gani na yi kamar sun yi mamaki kadan, abin takaici ne, ba sa mini kallon dan uwansu."

Duk da sukar da ya sha a kafar sada zumunta a lokuta mabambanta, ya ci gaba da bayyana kansa a matsayin kare tare da yin wasa irin na dabbobi.

Toco na neman masu tunani irin nasa

Da yake martani ga masu sukarsa, Toco ya ce:

"Ina takaicin yadda mutane ba sa tunanin haka. Ina son dabbobi kuma ina kaunar wasa dasu kamar dan uwansu. Wannan ne rayuwata don haka zan ci gaba da yi."

Kara karanta wannan

Dama-dama: Tinubu ya karawa ma'aikata albashi, amma akwai abin kura a gaba

A yanzu dai Toco na neman 'yan uwansa masu tunanin dabbobi domin ya zama abokinsu tare da yanke alaka da kasancewa dan adam.

Burinsa dai shine ya samu mutane masu tunani da kawa-zuci irin nasa don abokanci juna da wannan tunani irin na dabbobi.

Yadda lamarin ya faru

A baya, mun kawo muku rahoton yadda Toco ya bayyana aniyarsa ta kashe makudan kudaden domin ya siffantu da karnuka.

Ya kashe kudade wajen dinka tufar da ta maida shi sak kare, jama'a da dama a kafar sada zumunta sun yi mamaki.

Ba wannan ne karon farko da ake samun mutanen da ke tunani tosasshe kan sauya siffa ta jiki kamanceceniya da dabbobi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.