Jami’ar Amurka Ta Mallaka Masa Takardun Tinubu, Atiku Zai Sheka Kotun Koli da Karfinsa

Jami’ar Amurka Ta Mallaka Masa Takardun Tinubu, Atiku Zai Sheka Kotun Koli da Karfinsa

  • Kamar yadda kotu ta yi umarni, Jami’ar jihar Chicago (CSU) ta fitar da takardun karatun Bola Tinubu
  • Lauyoyin Atiku Abubakar sun karbi takardun da su ke sa ran yin amfani da su a gaban kotun koli
  • Wannan ya kawo karshen surutan da ake yi game da gaskiyar karatun sabon shugaban kasar Najeriya

Chicago - Jami’ar jihar Chicago da ke kasar Amurka, ta damkawa Atiku Abubakar takardun karatun shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Rahotanni daga Premium Times sun tabbatar da cewa lauyoyin ‘dan takaran shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar sun karbi takardun.

Hakan ya zo daidai da umarnin da wata kotu da ke zama a Arewacin Illinois ta bada umarni a baya.

TINUBU
Samfurin Digirin abokan karatun Bola Tinubu Hoto: @jacksonpbn
Asali: Twitter

Atiku v Tinubu a shari'ar zaben 2023

Alhaji Atiku Abubakar ya na sa ran yin amfani da wadannan takardu domin ya kafa hujja da su a kotun koli inda ake shari’ar zaben 2023.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyoyin Atiku su na bukatar gabatar da hujjojinsu gaban kotun kolin kafin ranar Alhamis idan har su na son kalubalantar nasarar Tinubu.

A yammacin Litinin, Phrank Shuaibu ya tabbatar da sun karbi takardun da su ke bukata game da katatun shugaban kasar daga jami’ar CSU.

Atiku Abubakar ya samu karin hujjoji

Baya ga takardun shaidar katatun mai girma shugaban kasa, jami’ar ta ba Atiku wasu takardun digirin da ta ba dalibanta a shekarar 1979.

Wani lauya wanda babban jami’i ne a makarantar, Jamar C. Orr ya sa hannu a takardun shaidar Tinubu wanda ke cike da sarkakiya.

Asiri zai tonu ko za a wanke Tinubu

Tinubu ya na ikirarin takardun karatunsa sun bace, sai ya gabatarwa INEC da wata shaidar difloma daga jami’ar ta CSU a matsayin madadinsu.

A takardar samun gurbin karatu. The Cable ta ce an bayyana Bola Tinubu a matsayin namiji, akasin zargin cewa ya yi amfani da sunan wata mata.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Atiku ya yi nasara kan Tinubu a kotun Amurka kan batun takardun digiri

Tsakanin takardar da Tinubu ya gabatar da samfurin da aka ba Atiku, ba a samu sabanin tambari ba, amma kwanan wata sun sha bam-bam.

Bukatarmu wajen Tinubu - Afenifere

Kwanakin baya rahoto ya zo cewa Shugaban Afenifere ya na ganin dole Bola Tinubu ya bi tafarkin Obafemi Awolowo kafin a samu cigaba a kasa.

Cif Ayo Adebanjo ya na so a bar kowane yanki ya gudanar da sha’aninsa yadda yake so, hakan zai rage ikon tarayya, ya karfafa jihohin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng