Bola Tinubu: Manyan Matsaloli Da Ke Zagaye Da Zababben Shugaban Kasa A Yayin Da Ya Cika Shekara 71

Bola Tinubu: Manyan Matsaloli Da Ke Zagaye Da Zababben Shugaban Kasa A Yayin Da Ya Cika Shekara 71

  • Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, yana murnar cika shekara 71 yau, 29 ga watan Maris, duk da cece-kuce kan shekarunsa
  • Kafin zamansa zababben shugaban kasar Najeriya, masu sukarsa sun tado batutuwa da dama game da shi, da dama cikinsu ba a gabatar da hujja ba
  • Wasu batutuwan da ake cece-kuce kansu dangane da shi sun hada da zargin alaka da miyagun kwayoyi, wacce ba a taba gabatarwa a kotun Najeriya ba

Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, zababben shugaban kasa, ya cika shekara 71 a yayin da ya ke murna a ranar Laraba 29 ga watan Maris.

A yayin da wasu shugabannin kasashe da fitattun mutane a Najeriya ke taya jigon na siyasan murna, yana da muhimmanci a yi rubutu dangane da manyan batutuwa game da shi.

Asiwaju Bola Tinubu
Bola Tinubu: Jerin wasu batutuwa da ake cece-kuce kansu game da zababben shugaban kasa. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

A shirye nake: Zababben gwamnan Katsina ya fadi abin da zai a ranar da ya karbi mulki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga dai wasu batutuwan kamar haka:

Shekara

Shekarun Tinubu na daya daga cikin abin da aka ti mahawara a kai a kansa. Wasu da dama suna ganin cewa ya fi shekarunsa na yanzu, yayin da wasu sau da yawa sun tafi shafinsa na Wikepedia suna canja labarai.

Tinubu a yau yana cika shekara 71 a duniya, ranar 29 ga watan Maris, a hukumance, amma cikin masu suka sun ce ya fi hakan tsufa.

Daya cikin irin wannan wallafar shine wanda 'Foundation of Investigative Journalism' ta yi inda ta ce shekarun zababben shugaban kasar ya kai 78.

Makaranta/Satifiket

Daya daga cikin batutuwan da ake cece-kuce a ka game da Tinubu shine makarantun da ya yi da satifiket din da ya ke da shi.

A hukumance, zababben shugaban kasar ya yi karatu a St John Primary School a Legas da Children's Home a Ibadan.

Kara karanta wannan

Riya ne: Saudiyya ta fusata, ta fadi abin da za ta yiwa masu daukar hoto a lokacin Hajji da Umrah

Ya yi karatun sakandare a Richard J Daley College a Chicago, Illinois, USA sannan ya yi jami'arsa a Chicago State University, Illinois, USA.

Ainihin Suna

Cikin masu sukar Tinubu akwai wadanda ke ganin ba ainihin sunansa ba kenan kuma ba daga iyalan Tinubu ya ke ba kamar yadda ya yi ikirari.

Amma, iyalinsa sun fito sun karyata hakan suna mai cewa sunansa Bola Ahmed Adekunle Tinubu.

Zargin harkalla da miyagun kwayoyi

Babban abin da ya fi janyo cece-kuce game da Tinubu shine batun alakarsa da miyagun kwayoyi.

Amma, masu zarginsa kawo yanzu ba su riga sun kallubalance sa a kotu don tabbatar da zarginsu ba sai dai tattauna abin a kafafen watsa labarai, wanda ana ganin hakan wani yunkuri ne na kawo cikas ga siyasarsa.

Obi da Obasanjo sun hadu a filin tashin jirage na Anambra, sun tattauna

A bangare guda, kun samu rahoton cewa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP a zaben watan Fabrairu, ya gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a filin tashin jirage na Awka, a jihar Anambra.

Kara karanta wannan

A kalla Rayuka 11 ne Suka Salwanta a Wasu Hadururruka Daban-Daban a Niger

Asali: Legit.ng

Online view pixel