Shugabannin Yarabawa Sun Yi taro a Legas, Sun Aikawa Bola Tinubu Sako a Abuja

Shugabannin Yarabawa Sun Yi taro a Legas, Sun Aikawa Bola Tinubu Sako a Abuja

  • An gudanar da taron shekara-shekara na GOAL a Legas, jagororin Yarbawa sun samu halarta
  • A jawabinsa, Cif Ayo Adebanjo ya ce babu ta yadda za a cigaba sai an canza tsarin tafiyar da mulki
  • Tsohon ya ba gwamnatin Bola Tinubu ta sauya salon mulki ta yadda shiyyoyi za su samu iko a doka

Lagos - An yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi kokari wajen ganin an ba shiyyoyi gashin kansu, a bar yankuna su iya tsayawa da kafafunsu.

Ba kowa ba ne su ka yi wannan kira ba illa shugabannin Yarbawan kasar nan ta karkashin shugaban kungiyar Afenifere, Cif Ayo Adebanjo.

A cikin makon nan ne Daily Trust ta rahoto Ayo Adebanjo ya yi jawabi a wajen taron GOAL na wannan shekarar da aka gudanar a garin Legas.

Kara karanta wannan

Babu Wani Uzuri, Zan Yaki Manyan Matsalolin Najeriya Har Abada - Shugaba Tinubu

Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a ofis Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Yarbawa sun yi taron GOAL a Legas

An yi wa taron bana take a kan hadin kan yankin kudu maso yamma a karkashin inuwar VOR.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jagoran na ‘yan Afenifire ya na cikin wadanda su ka gabatar da jawabi, har ya tuna da kokarin da Marigayi Obafemi Awolowo ya yi a lokacinsa.

Adebanjo ya ce Obafemi Awolowo ya yaki tsarin da turawan tsarin mulkin mallaka su ka zo da shi.

Dole Tinubu ya bi tafarkin Obafemi Awolowo

Dattijon ya na ganin cewa idan ba a bar kowa ya ci gashin kan sa ba, za samu rashin cigaba a Najeriya, don haka ya yi kira da gwamnati mai-ci.

Adebanjo ya ankarar da Bola Ahmed Tinubu cewa duka shawarwarin da Awolowo ya kawo su na nan har yau, kuma za a iya aiwatar da su a kasar.

Kara karanta wannan

Ana Binciko Mutanen da ke da Alaka da Emefiele a Badakalar Naira Tiriliyan 7 a CBN

Obafemi Awolowo ya fadawa turawan mulkin mallaka cewa ba za su iya yin mulkin bai-daya a kasar nan ba.

Ya kamata sabon shugaban kasa ya canza tsarin mulkin tarayya ta yadda za a bar kowa ya tafi a yadda yake so.

Yarbawa babu hadin kai a Najeriya

Shugaban kungiyar DAWN da aka kafa domin cigaban Yarbawa, Mista Seye Oyeleye ya koka a game da rashin hadin-kai da yake damun kabilarsu.

Sun ta rahoto Oyeleye ya na cewa a yau mutanensa su na yi wa juna kallon jihohin da su ka fito, hakan ya kai ana jin haushi wajen rabon mukami.

Yaki da rashin gaskiya a Kano

Idan aka dawo yankin Arewa, an samu labari Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin ayi gaggawar dakatar da shugaban Hukumar KASCO.

Ana zargin Dr. Tukur Dayyabu Minjibir da saida whatsin gwamnatin jihar Kano, a yunkurinsa na yakar rashin gaskiya, gwamna ya dakatar da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel