Kasar Nijar Na Zargin Faransa Da Shuka Musu Sharri Wurin Hada Su Fada Da ECOWAS

Kasar Nijar Na Zargin Faransa Da Shuka Musu Sharri Wurin Hada Su Fada Da ECOWAS

  • Yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar tsakanin ECOWAS da Nijar, shugaban sojin kasar ya tona asiri
  • Abdourahamane Tchiani wanda ke jagorantar kasar ya ce Allah ba zai bar masu shuka musu sharri ba a kasar
  • Ya ce kasar Faransa ce ke musu sharri kala-kala don kara hada su da kungiyar ECOWAS da ke Yammacin Afirka

Yamai, Nijar – Shugaban sojin Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tchiani ya bayyana cewa sun gane munafurcin da kasar Faransa ke musu.

Tchiani ya ce duk munafurcin kasar Faransa kan hada su da kungiyar ECOWAS su na sane don haka za su dauki mataki.

Nijar na zargin Faransa da kulla sharri wurin ECOWAS
Kasar Nijar Na Zargin Faransa da Shuka Musu Sharri. Hoto: A. Tchiani, Emmanuel Macron.
Asali: Facebook

Wane zargi Nijar ke yiwa Faransa kan ECOWAS?

Shugaban ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na kasar inda ya ce wane riba kasashen Senegal da Najeriya da sauran kasashen za su samu idan Nijar ta shiga matsala.

Kara karanta wannan

Muhammadu Buhari: Babban Sakona Ga Mutanen Najeriya a Ranar Murnar 'Yancin Kai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa ta’adanci da ke damunsu ma kakaba musu aka yi inda wadanda su ka kawo shi ba za su bar nufinsu ba duk da sun bar kasar, TRT Hausa ta tattaro.

Ya ce:

“Allah ba zai bar wadanda su ka shuka mana sharri ba kuma zai saka mana saboda sun ci amanarmu.
“Faransa ta na da wata mummunar manufa amma ta fahimci zuwanmu zai kawo mata cikas wurin cimma wanna manufa.”

Tchiani ya ce sojin Faransa na daf da watsewa daga kasar nan ba da jimawa ba.

Ya kara da cewa:

“Sojojinsu na kan hanyar tafiya, da yardar Allah za su bar kasar kawai lokaci su ke jira.”

Wane sako Nijar ta tura ga Faransa?

Dangane da mu’amala tsakanin kasashen biyu, Tchiani ya ce duk yadda Faransa ta ga dama haka za a yi amma maganan tattalin arziki Nijar ce ke da iko.

Kara karanta wannan

Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo da ‘Biliyan 50’, Gwamnatin Tinubu

Ya ce arzikin Nijar na ‘yan Nijar ne saboda su na da ‘yanci na tabbas ba na baki ba wanda za su juya tattalin arzikinsu, Al Mayadden English ta tattaro.

A karshe, Janar Tchiani ya godewa kasashen Mali da Burkina Faso kan irin gudumawa da su ke ba su.

Tchiani ya yi magana ne musamman kan bude iyakoki da kasashen su ka yi bayan Najeriya ta rufe iyakokinta.

Ya ce idan kasashen Mali da Burkina Faso ba su yi musu wannan kara ba da yanzu ba su san inda su ke ba.

Faransa ta zargi sojin Nijar da garkuwa da jakadanta

A wani labarin, kasar Faransa ta zargi sojin Jamhuriyar Nijar da garkuwa da jakadanta a kasar.

Shugaba Emmanuel Macron shi ya yi wannan zargi inda ya ce jakadan ba ya samun abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.