Cinikin bayi: Wasu kalaman Gaddafi sun fara zama gaskiya

Cinikin bayi: Wasu kalaman Gaddafi sun fara zama gaskiya

- Kalaman tsohon shugaban kasar Libya ta fara bayyana

- Marigayi Gaddafi ya ce kasashen Turai basu fi shi son Afrika ba

- Tsohon shugaban ya ce idan Afrika ta ba da hakin kai aka kashe shi, za su sake dawo da kasuwar bayi a Afirka

A shekara ta 2009 ne tsohon shugaban kasar Libya, Muammar Gaddafi ya yi wani jawabi inda yake jawo hankalin al’ummar Afrika akan makircin kasashen Turai.

Gaddafi ya yi jawabin kamar haka, "Idan kuna tunanin kasashen Turai sun fini son Afirka, to ku basu hadin kai su kasheni, zaku ga yadda za su sake dawo da kasuwar bayi a Afirka".

A gaskiyar magana marigayi Gaddafi ya yi angen nisa kuma ya san abunda ya tarewa turawa a kasar sa Libya. Yanzu haka gashi bayan ransa kasuwancin bayi da bautar da bakaken fata ya dawo a kasar Libya.

Cinikin bayi: Wasu kalaman Gaddafi sun fara zama gaskiya
Wasu daga cikin kalaman tsohon shugaban kasar Libya, Muammar Gaddafi

Idan dai baku manta ba a karshen makon nan ne Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban kasar Chadi, Idris Derby ya fitar da wani sanarwa a kan cinikin bayi da azabtar da bil'adama da mahukuntan kasar Libya suke yi a halin yanzu.

KU KARANTA: Matakin da ya dace akan Libya game da zargin cinikin bayi da bautar da mutane

Yayin da shugaban ya baiwa mahukuntan Libiya wa'adin awanni 24 a kan su saki duk wani bakar fata da suke rike da su a matsayin bawa ko wadanda suka kama a lokacin da suke kokarin tsallaka tekun Libya zuwa nahiyar turai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng