Gwamnatin Tinubu Ta Ayyana Ranar Litinin a Matsayin Hutun Ranar ’Yancin Kai

Gwamnatin Tinubu Ta Ayyana Ranar Litinin a Matsayin Hutun Ranar ’Yancin Kai

  • Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba a matsayin hutun ranar 'yancin kai
  • Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis
  • Ministan ya kuma taya yan Najeriya na gida da waje murnar bikin ranar 'yanci

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu don bikin cikar Najeriya shekaru 63 da samun yancin kai.

Olubunmi Tunji-Ojo, wata sanarwa da ministan harkokin cikin gida ya yi a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba a madadin gwamnatin tarayya, ya ayyana Litinin, 2 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu, rahoton The Nation.

Gwamnatin tarayya ta ba da hutun ranar 'yancin kai
Gwamnatin Tinubu Ta Ayyana Ranar Litinin a Matsayin Hutun Ranar ’Yancin Kai Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ministan Tinubu ya taya ‘yan Najeriya murnar samun ‘yancin kai

A cikin sanarwar tasa, ministan ya taya ‘yan Najeriya na gida da waje murnar samun ‘yancin kai.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Wike ya kori manyan jami'an hukumomi da kamfanonin FCTA

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin sanarwar da ke dauke da sa hannun sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Oluwatoyin Akinlade, ministan ya bayyana jajaircewar gwamnatin tarayya na tunkarar kalubalen da ke addabar kasar.

Sanarwar ta ce:

"Sanannen abu ne a yau cewa matsalolin tattalin arziki da tsaro abu ne da suka addabi duniya, kuma ba a ware Najeriya ba."

Ministan harkokin cikin gida ya yi magana kan kokarin gwamnati

Ya kara da cewar gwamnati na kokari don dakile tarin kalubalen da ke tunkarar kasar kuma za ta ci gaba da yin hakan har sai an samu sauki a kasar, rahoton Daily Trust.

Tunji-Ojo ya jaddada cewa babban matsayin Najeriya a kasashen duniya da ci gaban da ke tunkaro kasar abu ne da za a iya cimmawa idan muka yi aiki tare cikin hadin kai.

Kara karanta wannan

Masani Ya Hasko Abubuwan Da Za Su Jawo Kayan Abinci Su Yi Masifar Tsada a Najeriya

A cewar ministan, Najeriya za ta ci gaba da zama abin alfaharin Afirka, kuma za ta kasance wani ginshiki ga ajandar Shugaba Bola Tinubu.

Bikin Maulidi: Gwamnan Jigawa ya tsawaita hutu zuwa ranar Alhamis

A wani labarin, mun ji cewa Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ayyana ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba a matsayin hutu domin bikin Maulidi na 2023.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, jami'in hulda da jama'a na ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 27 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng