Kungiyar TUC Ta Ba Tinubu Makonni 2 Don Kammala Tattaunawa a Kan Cire Tallafin Mai

Kungiyar TUC Ta Ba Tinubu Makonni 2 Don Kammala Tattaunawa a Kan Cire Tallafin Mai

  • Kungiyar kwadago ta ba gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu sabon wa'adi
  • Kungiyar TUC ta ba FG wa'adin makonni biyu ta kammala duk wasu tattaunawa da take yi a kan cire tallafin man fetur
  • A halin da ake ciki, TUC ta ce dole a magance duk wasu batutuwa da ke kasa kafin a cimma yarjejeniya kan tsarin da za a amince da shi a matsayin na rage radadin cire tallafin mai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

An baiwa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sabuwar sanarwa dangane da tattaunawa a kan cire tallafin man fetur.

Yayin da yan Najeriya ke jiran sakamakon tattaunawa tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin tarayya kan matakan rage radadin da cire tallafin man fetur , kungiyar TUC ta yi barazanar fara yajin aiki na gama gari.

Kara karanta wannan

Yadda Muhammadu Buhari Ya Ƙara Kuɗin Makarantu, Ya Ƙyale Tinubu da Shan Suka

Kungiyar kwadago ta ba Tinubu mako 2 kan cire tallafin mai
Kungiyar TUC Ta Ba Tinubu Makonni 2 Don Kammala Tattaunawa a Kan Cire Tallafin Mai Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Cire tallafin mai: TUC ta yi barazanar tafiya yajin aiki idan gwamnatin Tinubu ta ki yin abun da ya dace

Kamar yadda jaridar ThisDay ta rahoto, TUC ta baiwa gwamnatin tarayya makonni biyu masu zuwa don cimma matsaya kan tattaunawar da ke gudana ko kuma a fuskanci yajin aiki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Musamman, kungiyar ta ce idan har gwamnatin Tinubu bata yi wani kwakkwaran abu ba bayan 19 ga watan Agusta, za ta dauki mataki don kare ma'aikata da al'ummar kasar daga mawuyacin hali mara karewa, rahoton Vanguard.

Kungiyar TUC ta bukaci kayan rage radadi

Baya ga fara rage yawan kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da harkokin mulki, kungiyar ta ce ya kamata gwamnatin tarayya da na jihohi su samar da ingantattun kayan rage radadi wadanda za a iya tabbatar da su sannan a aiwatar da su a lokacin da aka tsara.

Kara karanta wannan

Tsadar Man Fetur: Kungiyar CAN Ta Ba Shugaba Tinubu Muhimmiyar Shawara Kan Tallafin Da Zai Bayar

Kakakin majalisar wakilai zai gana da Tinubu kan yajin aikin da likitoci ke shirin tafiya

A wani labarin, mun ji cewa kakakin majalisar wakilai, Honourable Tajudeen Abbas, na shirin ganawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa ganawar da za a yi tsakanin Abbas da shugaban kasar na daga cikin kokarin da ake yi na dakile shirin da kungiyar likitocin Najeriya (NARD) ke yi na shiga yajin aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng