Zamfara: Gwamna Lawal Ya Zargi Hukumomin FG Da Tattaunawa Da Yan Ta'adda

Zamfara: Gwamna Lawal Ya Zargi Hukumomin FG Da Tattaunawa Da Yan Ta'adda

  • Gwamna Lawal ya faɗi mutanen da yake zargi daga FG sun fara tattaunawar sulhu da 'yan bindiga a jihar Zamfara
  • Dauda Lawal na PDP ya koka da matakin wanda ake zargin wasu hukumomin FG sun ɗauka ba tare da sanin gwamnatin jihar ba
  • Ya kuma jaddada matsayarsa cewa gwamnatinsa ba zata tattauna da 'yan bindiga ba domin a baya an yi amma babu sakamako mai kyau

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya na tattaunawar sulhu da ‘yan ta’adda a jihar ba tare da saninsa ba.

Gwamna Lawal, mamban jam'iyyar adawa ta People's Democratic Party (PDP), ba ya goyon bayan tsarin tattaunawar neman zaman lafiya da 'yan bindiga a jihar Zamfara.

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal.
Zamfara: Gwamna Lawal Ya Zargi Hukumomin FG da Tattaunawa da Yan Ta'adda Hoto: Dauda Lawal Dare
Asali: Facebook

Ya ce yana da rahoton cewa ana tattaunawa da wasu ‘yan ta’adda a kananan hukumomi daban-daban na jihar Zamfara, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Muna da Hujjoji" Gwamna Lawal Ya Maida Zazzafan Martani Ga Gwamnatin Tinubu Kan Zaman Sulhu da 'Yan Bindiga

Gwamnan ya yi kira da a gudanar da cikakken bincike kuma mai zurfi kan abin da ya kira tattaunawar sirri da aka yi da ‘yan bindiga.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Idris, ya fitar, an ji Lawal na cewa:

"Mun samu wasu rahotanni da ke nuna wata tawaga ta fara tattaunawa da ƙungiyoyin 'yan ta'adda ba tare da sanin gwamnatin jiha ba, kuma ana zargin hukumomin gwamnatin tarayya ne suka turo su."

Lawal ya koka da matakin da wasu hukumomin FG suka ɗauka na tattaunawa da ‘yan bindiga ba tare da jin ta bakin gwamnatin jiha da sauran hukumomin tsaro ba.

“Gwamnatin Zamfara ta samu rahoton yadda wasu tawagar FG suka gana da kungiyoyin ‘yan bindiga daban-daban a garuruwan Birnin Magaji, Maradun, Mun haye, Ajah, Bawo, da Bagege."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Yi Magana Mai Kyau Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a Zaɓen 2023

“Gwamnatocin da suka shuɗe ba su cimma sakamako mai kyau ba yayin da suka tattauna da ‘yan bindiga. Dole mu ɗauki darasi daga kura-kuran da aka yi a baya, mu lalubo sabuwar hanya don dawo da zaman lafiya a Zamfara.”

Mai magana da yawun gwamnan ya jaddada matsayar Lawal na cewa gwamnatinsa ba za ta tattauna da ‘yan ta’adda da nufin neman sulhu ba, This Day ta tattaro.

Akwai Alamun Tambaya Kan Wasu Yan Siyasa Game da Kashe-Kashen Filato, Mutfwang

A wani rahoton na daban Gwamnan jihar Filato, Celeb Mutfwang, ya tona waɗanda yake zargi da hannu a ta'addancin da ake aikata wa a jiharsa.

Ya yi bayanin cewa babu wata ƙabila da ke yaƙar abokiyar zamanta a jihar Filato , sai dai wasu bara gurbi da aka ɗauko haya domin su haɗa mutane faɗa su tada zaune tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel