Shugaban Matasa da Hadiman Gwamnan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Bayelsa

Shugaban Matasa da Hadiman Gwamnan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Bayelsa

  • Gwamnan jihar Bayelsa na jam'iyyar PDP ya ƙara rasa manyan makusanta yayin da ake tunkarar zaben gwamna a watan Nuwamba
  • Masu baiwa gwamna Diri shawara ta musamnan 3 da shugaban matasan PDP sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC
  • Ɗan takarar gwamna na APC ya yaba musu bisa ɗaukar wannan mataki wanda ya nuna sun fi son ci gaban jihar fiye da aljihunsu

Jihar Bayelsa - Tsagin gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, mai neman ta zarce a zaɓen watan Nuwamba, 2023 ya ƙara samun tasgaro ranar Litinin, 18 ga watan Satumba.

Jaridar Punch ta rahoto cewa hakan ta faru ne yayin da wasu daga cikin hadiman gwamna na kusa-kusa da shugaban matasan PDP, Nunieh Odede, suka sauya sheƙa zuwa APC.

Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa.
Shugaban Matasa da Hadiman Gwamnan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Bayelsa Hoto: Douye Diri
Asali: Facebook

Odede ya sanar da murabus daga muƙaminsa na shugaban matasa a wata wasiƙa da ya rubuta da hannu yayin da hadiman gwamnan suka aje muƙamansu suka koma bayan Timipre Sylva na APC.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Na Kusa da Atiku Abubakar Ya Tona Asirin Gwamnatin Shugaba Tinubu Kan Abu 1 Tal

A wata sanarwa da mai magana da yawun Sylva, ɗan takarar gwamna a inuwar APC, Julius Bokoru, ya tabbatar cewa Odede da sauran masu sauya sheƙar sun gana da ubangidansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana sunayen makusantan gwamna Diri na jihar Bayelsa, waɗanda suka bar bangarensa kana suka koma bayan Sylva yayin da ake shirin tunkarar zaɓe, jaridar Independent ta rahoto.

Makusantan gwamna Diri da suka koma APC

Masu sauya sheƙar sun haɗa da shugaban hukumar tsaftace mahalli ta jiha, Abiah Oyisor, da masu bada shawara kan ayyuka na musamman su 3, Itu Goodluck, Timipa Ile da Olali Suwofien.

Haka zalika wakilin gwamna na musamman a ƙaramar hukumar Yanagoa, Ayaye Obuma, na cikin waɗanda suka sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Sanarwan ta haƙaito Sylva na yaba wa Odede da sauran jiga-jigan bisa kwarin guiwar zaɓen ci gaban jihar Bayelsa fiye da son zuciyarsu.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Maida Martani Mai Jan Hankali Kan Hukuncin Kotu Na Sahihancin Zaɓen Gwamna

A rahoton Pulse, an ji Sylva na cewa:

"Matasa su ne ginshiƙin kowace al’umma, matasa ne suke jan ragamar yadda al'umma zata kasance. Matakin da kuka ɗauka a yau jarumtaka ne da rashin son kai."

Gwamnatin Tinubu Na Kulla Yadda Za a Kama Ni a Tsare, Hadimin Atiku

A wani rahoton kuma Makusancin Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ƙulla yadda za a damƙe shi a garkame.

Daniel Bawal ya ce wasu sahihan bayanan sirri da ya samu daga Aso Villa, sun nuna ana shirin sa jami'an tsaro su yi ram da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262