Akwai Yiwuwar a Samu Sauki Yayin da Farashin Kayayyakin Abinci Suka Yi Faduwar Warwas a Jihar Taraba

Akwai Yiwuwar a Samu Sauki Yayin da Farashin Kayayyakin Abinci Suka Yi Faduwar Warwas a Jihar Taraba

  • An naqalto yadda kayayyakin abinci suka fara sauka a wasu jihohin Arewacin Najeriya yayin da damina ke shirin karewa
  • Damina ta yi albarka, buhun masara dya koma tsakanin N20,000 zuwa N28,000 a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas
  • 'Yan Najeriya na ci gaba da kuka kan yadda kayayyakin rayuwa suke kara tashi tare da samun tsaiko a yanzu

Jihar Taraba - Rahoton da muke samu daga jaridar Aminiya ya bayyana cewa, amfanin gona ya fara sauka a wasu jihohin Najeriya, musamman Taraba.

Binciken da aka yi ya nuna cewa, daminar bana ta yi kyau ainun, don haka akwai yiwuwar a samu saukin kayayyakin abinci a kasar nan.

Majiya ta shaida cewa, an smau damina mai albarka a dukkan kananan hukumomi 16 na jihar da ke Arewa maso gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Bindiga Sun Tarwatsa Garuruwan Noma 15 a Arewa, Sun Raba Mutane da Amfanin Gonakinsu

Yadda kayan abinci ya sauka a Arewa
Kayan abinci a Najeriya | Hoto: NBS
Asali: Facebook

An fara girbin kayan abinci

An naqalto cewa, tuni jama'a suka fara girbin masara, shinkafa, doya, dankali, gero, rogo da ma wake da dai sauran kayayyaki a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A halin da ake ciki, an ce buhin hatsi, kamar masara bai wuce N20,000 zuwa N28,000 ba a kasuwanni sabanin yadda aka siyar kusan N60,000 a kwanakin baya.

Yayin da a tsakiyar shekarar nan aka siya babban buhun gero a kan kudi N28,000 ko sama, a yanzu bai wuce N14,000 ba.

Haka nan, an ce farashin gero da doya da shinkafa ma a barsu a baya ba, domin sun yi saukar ban mamaki a jihar.

Daga bakin mai sarin shinkafa a Taraba

Umar Inuwa, wani dan kasuwa a jihar Gombe da ke zuwa jihar Taraba sarin shinkafa ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa, tabbas kayayyaki sun sauka.

Kara karanta wannan

Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Kai Naira Tiriliyan 87, An Fadi Abinda Kowane Dan Ƙasa Zai Biya

A kalamansa:

"Duk da ban je sari ba a makon nan, amma tabbas wadanda muke hulda dasu sun ce kaya ya sauka kuma wannan ne mafari.
"Muna sa ran abinci ya yi araha nan ba da jimawa da yardar Allah. Fatan Allah ya saukake mana rayuwa."

Za a samu saukin kayan abinci

A bangare guda, Gwamnatin Tarayya za ta dauki mataki a kan kungiyoyin ‘yan kasuwa saboda zargin kara farashin kaya babu dalili.

Hukumar Gasa da Kare Hakkin Kwastomomi (FCCPC) ita ta bayyana haka ta bakin shugaban hukumar, Babatunde Irukera a ranar Talata 18 ga watan Yuli.

Ya ce suna kara farashin kayayyaki da kuma tsare-tsare da kungiyoyin suke kawo wa wanda ke hana gasa a tsakanin ‘yan kasuwa, TheCable ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel