CBN Ya Ce Babu Batun Sauya Fasalin Naira Domin Ya Dawo Daidai Da Dalar Amurka

CBN Ya Ce Babu Batun Sauya Fasalin Naira Domin Ya Dawo Daidai Da Dalar Amurka

  • Babban Bankin Najeriya (CBN), ya musanta raɗe-raɗin da ake yi na cewa yana yunƙurin daidaita naira da dala
  • Bankin ya fadi hakan yayin martani kan rahoton da ke cewa yana yunkurin maida dala 1 daidai da naira 1.25
  • Haka nan CBN ya bukaci al'umma da su yi watsi da labarin domin kuwa ba shi da tushe balle makama

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN), ya musanta raɗe-raɗin da ake yayatawa a kafafen sada zumunta, kan cewa yana yunƙurin dawo da naira daidai da dalar ƙasar Amurka.

Bankin na CBN dai ya yi wannan martani ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, 13 ga watan Satumba.

CBN ta musanta batun sauya fasalin naira
CBN ya ce ba gaskiya ba ne batun dawo da dalar Amurka daidai da naira. Hoto: @Nairarates
Asali: Getty Images

CBN ya musanta batun sauya fasalin naira

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: Yadda Wata Kada Ta Mayar Da Wata Baiwar Allah Mai Kafa Daya Bayan Taje Rafi

A cikin saƙon da ya yaɗu a kafafen sada zumunta na zamani, an bayyana cewa za a dawo amfani da kuɗaɗe na sulalla da aka yi amfani da su a baya, sannan a rage girman waɗanda ake amfani da su a yanzu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu yada labaran sun nuna cewa daga watan Janairun shekarar 2024 sabbin sauye-sauyen za su fara aiki ba tare da ɓata lokaci ba.

Sai dai bankin na CBN a cikin saƙon da ya wallafa, ya bayyana cewa labarin duk na ƙarya ne, inda ya buƙaci al'umma su yi watsi da shi.

Najeriya za ta koma amfani da dala? Gaskiya ta fito

Legit Hausa a baya ta yi rahoto kan musanta labarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa Najeriya za ta koma amfani da dalar Amurka a matsayin kuɗin hada-hada.

Kara karanta wannan

"Ban Taɓa Ganin Naira Biliyan 1 a Asusun Banki Na Ba Har Na Bar Mulki" Tsohon Gwamnan Arewa

Gidan talabijin na Arise, wanda shi ne aka alaƙanta bidiyon da shi ne ya fitar da wani sako ta shafinsa na manhajar X, inda ya nesanta kansa da bidiyon.

Haka nan Legit Hausa ta gudanar da bincike diddiƙi a kan bidiyon, inda binciken ya nuna cewa wasu ne kawai suka haɗa bidiyon, amma a zahirance abinda ke ciki ba gaskiya ba ne.

Tinubu ya gaza biyan bashin tiriliyan 87 da ake bin Najeriya

Legit Hausa a baya ta yi rahoto kan sununun bashi har na naira tiriliyan 87 da ake bin Najeriya wanda ake tsammanin Shugaba Bola Tinubu zai biya a wa'adin mulkinsa.

An bayyana cewa ƙasar China kaɗai, na bin Najeriya bashin da ya kai na dala biliyan huɗu da ɗigo talatin da huɗu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel