Sanata Kalu Ya Lallasa Jam'iyyar PDP da Labour Party a Kotun Zabe

Sanata Kalu Ya Lallasa Jam'iyyar PDP da Labour Party a Kotun Zabe

  • Sanata Kalu na jam'iyyar APC ya samu nasara kan PDP da Labour Party yayin da Kotun zaɓe ta yanke hukunci ranar Talata
  • Kotun zaben NASS ta tabbatar da nasarar tsohon gwamnan jihar Abia a matsayin halastaccen sanatan Abia ta arewa
  • Alkalan Kotun sun haɗa baki sun yi fatali da kararrakin 'yan takarar jam'iyyar PDP da na jam'iyyar LP bisa rashin cancanta

Abia - Kotun sauraron ƙararrakin zaben majalisar tarayya ta tabbatar da nasarar Sanata Orji Uzor Kalu na jam'iyyar APC mai wakiltar mazaɓar Abia ta Arewa.

Kwamitin Alkalai uku ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Samson Paul-Gang ne suka yanke hukuncin da baki ɗaya ranar Talata, 12 ga watan Satumba, 2023.

Sanata Orji Uzor Kalu.
Sanata Kalu Ya Lallasa Jam'iyyar PDP da Labour Party a Kotun Zabe Hoto: Senator Orji Uzor Kalu
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Alƙalan sun yi fatali da ƙarar ɗan takarar jam'iyyar PDP, Mao Ohuabunwa, da na Labour Party, Nnamdi Iro Orji, saboda rashin cancanta.

Kara karanta wannan

Kotun Zaben NASS Ta Tsige Ɗan Minista Daga Kujerar Ɗan Majalisar Tarayya, Ta Ba Da Sabon Umarni

Kotun, yayin da take tabbatar da nasarar Kalu na jam’iyyar APC ta ce zaben tsohon jagoran majalisar dattawa ya cika sharuɗɗan tanade-tanaden dokar zabe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kotu ta kori kararrakin PDP da LP

Alkalan Kotun sun kuma yi fatali da hujjar masu shigar da kara cewa zaɓe bai gudana ba a rumfunan zabe sama da 120 musamman a kananan hukumomin Ohafia da Arochukwu.

Nnamdi Iro da Ohuabunwa da suka zo na biyu da na uku, sun bukaci kotu ta soke zaben tsohon gwamnan Abia bisa zargin saɓa wa kundin dokoki

Har ila yau, Kotun ta kori ƙorafin PDP da LP cewa adadin wadanda suka yi rajista a rumfunan zaben da abun ya shafa sun haura tazarar ƙuri'u tsakanin Kalu da wanda ya zo na biyu.

Kotun ta kuma tabbatar da cancantar Kalu na tsayawa takara tare da bayyana cewa kotun koli ta soke hukuncin da aka yanke masa a baya, Ripples ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Zaben NASS Ta Tsige Ƙarin 'Yan Majalisun Tarayya 2, Ta Ba APC da APGA Nasara

Baturen zaɓen INEC na mazaɓar Abia ta Arewa, Mista Chinedu Nnamdi, ya bayyana Kalu, jigo a APC a matsayin wanda ya lashe zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Shugaba Tinubu Ya Bada Umarnin Bincike Kan Yawaitar Hatsarin Jirgin Ruwa a Najeriya

A wani labarin kuma Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumar da ke kula da tsaron ruwa ta gudanar da bincike kan haɗurran jiragen ruwan da suka faru.

Shugaban kasan ya kuma jajantawa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon ibtila'in tare da tabbatar da kare irin haka nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel