“Kada Ku Kuskura Ku Bar Matayenku Ku Tafi Turai”: Dan Najeriya Da Ke Zaune a UK Ya Gargadi Ma’aurata

“Kada Ku Kuskura Ku Bar Matayenku Ku Tafi Turai”: Dan Najeriya Da Ke Zaune a UK Ya Gargadi Ma’aurata

  • Wani dan Najeriya ya gargadi yan uwansa maza a kan tafiya turai suna barin matayensu a gida
  • A wani bidiyo da ke yawo a TikTok, ya nuna adawa da shawarar sannan ya yi gagarumin gargadi ga maza
  • Yayin da mutane da dama suka goyi bayan matsayinsa, wasu sun caccaki shawarar da ya bayar sannan suka ba da labarin tafiyarsu turai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani dan Najeriya mai suna @odogwukiwi a TikTok ya aika gagarumin gargadi kan dabi'ar barin mata a gida don tafiya wata kasar.

A cikin bidiyon, Odogwukiwi ya nuna damuwarsa, yana mai bayyana cewa yana da matukar hatsari barin matar mutum a gida yayin da ya shi zai tafi turai.

Matashi ya gargadi maza kan tafiya turai su bar matansu a gida Najeriya
“Kada Ku Kuskura Ku Bar Matanku Ku Tafi Turai”: Dan Najeriya Da Ke Zaune a UK Ya Gargadi Ma’aurata Hoto: @odogwukiwi/TikTok.
Asali: TikTok

Wani mutum ya shawarci maza kan barin matayensu yayin da za su tafi turai

A cikin bidiyon, ya yi ikirarin cewa mata wadanda mazajensu suka koma turai ba za su ci gaba da zama masu gaskiya a garesu ba.

Kara karanta wannan

"Ba Za Ki Fito a Kowani Hoto Ba": Mai Hoto Ya Yanke Kanwar Amarya Daga Hotunan Biki Saboda Ta Ki Ba Shi Shinkafa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kana shirin barin matarka a Naija don tafiya turai, ka tambaye ni me za ka yi don kada maza su dunga kallonta. Kamar dai kana shan wiwi ko? Ka bar mata a Najeriya ka tafi turai kamar dai ka bar doya ne a hannun akuya, ka zo kana mamakin wai akuya ya cinye doya.
"Barin mata a Najeriya kamar dai ka paka motarka a wurin jama'a ne. Kai ka yi kasada! idan ka tambayeni wannan shirmen kuma, zan jefe ka da abun rubutu koda dai ina bukatarsa."

Jama'a sun yi martani yayin da wani ya shawarci maza da kada su bar matansu a gida su tafi Turai

Bidiyon ya lissafo kalubale da hatsarin da mutane za su iya fuskanta idan suka tafi suka bar matansu a gida yayin da suka tafi turai.

Kara karanta wannan

Kwanaki 100 Kan Mulki: Tarun Matsaloli 3 Da Ke Hana Shugaba Tinubu Sakewa Tun Bayan Hawanshi Mulki

Jama'a sun fadi ra'ayoyinsu mabanbanta kan bidiyon wanda ya yadu a TikTok.

@AkuPowerOflmolly ya ce:

"Dan uwana ba dukka mata bane suka taru suka zama daya, duk da ban yarda da kowa ba amma na san muna da masu yan dama-dama, mungode."

@Petra ta yi martani:

"Ashe shiyasa suka kunsa mun ciki kafin su tafi."

@AdaHarford ta yi martani:

"Na tsaya da amana, zan iya fadin wannan a ko'ina, a kodayaushe. Ba a taru an zama daya ba."

@urchman06 ta yi martani:

"Magana ta gaskiya dan uwana."

Matashi ya baje kolin gidansa a Canada, yana biyan N778k duk wata

A wani labarin, mun ji cewa wani mutumi da ke zama a Canada ya zagaya da mutane cikin gida mai dakuna biyu da yake biyan N778k duk wata.

Mutumin mai suna Benny Tours Canada, ya wallafa bidiyon gidan wanda yake a yankin New Brunswick, Canada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel