Kungiyar NLC Ta Janye Yakin Aikin Gargadi Na Kwanaki 2 Da Su Ka Shiga

Kungiyar NLC Ta Janye Yakin Aikin Gargadi Na Kwanaki 2 Da Su Ka Shiga

  • Kungiyar Kwadago ta NLC ta bukaci ma'aikata da su koma bakin aiki bayan kammala yajin aiki
  • Kungiyar ta shiga yajin aiki na gargadi har na tsawon kwanaki biyu daga ranar Talata zuwa yau Laraba
  • Shugaban kungiyar, Joe Ajaero shi ya bayyana haka inda ya ce an samu biyan bukata yadda mutane su ka ba da hadin kai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta janye yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da ta shiga a wannan mako.

Kungiyar ta bukaci ma'aikata da dukkan mambobinta su koma bakin aiki a gobe Alhamis 7 ga watan Satumba kamar yadda su ka yi alkawari tun farko.

NLC ta janye yajin aikin gargadi na kwanaki biyu
Kungiyar NLC Ta Janye Yakin Aikin Gargadi A Yau. Hoto: Bola Ahmed Tinubu, NLC.
Asali: Twitter

Meye kungiyar NLC ke cewa kan yajin aiki?

A cikin wata sanarwa, shugaban kungiyar, Joe Ajaero ya yabawa ma'aikata yadda su ka ba su hadin kai inda ya ce an samu biyan bukata.

Kara karanta wannan

"Babu Dawowa Baya", Kashim Shettima Ya Tona Asirin Shirin Masu Handame Kudaden Tallafi, Ya Tura Gargadi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kungiyar ta shiga yajin aiki ne na gargadi na tsawon kwanaki biyu kan cire tallafin man fetur a kasar, cewar Channels TV.

Yajin aikin na kungiyar NLC ya gurgunta harkokin kasuwanci da kuma tattalin arziki.

Ajaero ya ce:

"Mu na mai sanar da ku cewa an samu ci gaba a yayin ganawa da masu ruwa da tsaki.
"Mu na gode muku da goyon bayan da ku ka bayar lokacin yajin aiki.
"Ya tabbata mun tura muhimmin sako ga gwamnati."

Wane roko NLC ta yi ga jama'a kan yajin aiki?

Ajaero ya ce tun da an samu abin da ake bukata ya roki ma'aikata da sauran jama'a da su koma bakin aiki kamar yadda su ka yi alkawari, cewar TheCable.

Ya kara da cewa:

"Yayin da mu ke kawo karshen yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da tsakar daren yau, ina rokonku da ku koma aiki gobe kamar yadda mu ka yi alkawari a farko."

Kara karanta wannan

"Ba Mu Ba Ne": Manoma Sun Yi Martani Bayan Tinubu Ya Umarci Bankin CBN Ya Kwato Tiriliyan 1 Na Lamuni, Bayanai Sun Fito

Kungiyar ta shiga yajin aikin ne saboda wahalhalu da 'yan Najeriya ke ciki bayan cire tallafin man fetur a kasar.

Kungiyar NLC Ta Shiga Yajin Aikin Gargadi Na Kwanaki 2

A wani labarin, Kungiyar Kwadago ta NLC za ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyu.

Wannan na zuwa ne bayan kungiyar ta nuna damuwa kan cire tallafin man fetur a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.