An Yi Wa Ango Da Amarya Kyautar Galan Babu Komai Ciki a Ran Aurensu, Bidiyon Ya Girgiza Intanet
- An bai wa wani mutum da amaryarsa kyautar galan babu komai ciki a matsayin gudunmawar biki, kuma bidiyon ya yadu a soshiyal midiya
- A cikin bidiyon, wani mahalarcin bikin ya tunkari ma'auratan sannan ya gabatar masu jarka kalar ruwan dorawa, lamarin da ya bai wa kowa mamaki
- Amarya da angon sun karbi gudunmawar baki a lekum, amma bidiyon ya haddasa cece-kuce a TikTok
Wani dan gayya a wajen biki ya gabatar da gudunmawar da ba a saba gani ba, kuma bidiyon ya yadu a TikTok.
A cikin wani dan gajeren bidiyo, mutumin ya tunkari amarya da ango dauke da wani galan mai kalar ruwan dorawa babu komai a cikinsa.
Matar da mijin nata sun karbi galan din baki a lekum, amma alamu sun nuna wannan kyauta ya bai wa amaryar mamaki.
Mahalarcin bikin ya gabatar da kyautar sannan ya tafi don bai wa sauran mutane damar gabatarwa sabbin ma'auratan nasu gudunmawar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An gabatar da galan babu komai ciki a matsayin gudunmawa a wajen biki
An gano amaryar da ango suna taka rawa bayan gabatar masu da kyaututtukan.
Wasu masu amfani da TikTok sun ce sun yi mamakin ganin irin wannan gudunmawar. Wasu sun tambaya ko da gaske mutumin ya je wajen bikin da galan babu komai ciki a matsayin gudunmawa. @fidoman87 ne ya wallafa bidiyon.
Kalli bidiyon a kasa:
Martanin yan TikTok yayin da wani ya gabatarwa amarya da ango galan babu komai
@valenciaborman ya ce:
"Galan babu komai a ciki. Hatta amaryar ta cika da mamaki."
@mishsherry ta yi martani:
"Shin wannan da gaske ne?"
Amarya ta fashe da kuka a wajen biki saboda rashin zuwa masu abinci
Halin Yunwa: Dalibi Ya Rasa Ransa Kan Zargin Rashin Wadataccen Abinci Mai Gina Jiki A Wata Makaranta Da Ke Jihar Kano
A wani labarin kuma, mun ji cewa wani mutumi mai suna @blogwithmcb a TikTok ya wallafa wani bidiyo mai tsuma zuciya inda yake lallashin wata amarya a wajen shagalin bikinta.
A cewar mutumin mai karamci, amaryar ta karaya yayin da masu abinci da ya kamata ace sun isa wajen bikin tun karfe 2:00 na rana suka ki zuwa har karfe 4:00 na yamma.
Ya ci gaba da karfafawa amaryar da ke zub da hawaye gwiwa, yana mai bata dalilai da za su sa ta farin ciki da fatan kammala taron bikin cikin nasara.
Asali: Legit.ng