Shugaba Tinubu Ya Magantu Kan Sabon Juyin Mulkin Sojoji a Gabon

Shugaba Tinubu Ya Magantu Kan Sabon Juyin Mulkin Sojoji a Gabon

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da sabon juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar Gabon
  • Tinubu ya nuna damuwarsa kan yadda juyin mulki ke yaɗuwa a Afirka, yana mai cewa ba zasu lamurci ci gaba da kwatar mulki da ƙarfin bindiga ba
  • Ya ce yana aiki tare da shugabannin ƙasahen ƙungiyar tarayyar Afrika domin ɗaukar mataki na gaba game da ƙasar Gabon

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar Gabon, yana mai cewa, "mulkin kama karya" yana yaduwa a fadin nahiyar Afirka.

Haka zalika Shugaba Tinubu ya bayyana matukar damuwarsa kan yanayin da ake ciki na dambarwar siyasa da zaman lafiya a kasar sakamakon hamɓarar da shugaba Ali Bongo.

Kara karanta wannan

Bidiyon Halin da Hamɓararren Shugaban Ƙasar Gabon Ke Ciki Ya Bayyana, Ya Aike da Saƙo Mai Muhimmanci

Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Magantu Kan Sabon Juyin Mulkin Sojoji a Gabon Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Shugaban ƙasa Tinubu ya ce a shirye yake ya yi aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran shugabannin ƙasashen nahiyar Afirka domin kare Demokuraɗiyya, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Tinubu ya faɗi haka ne a martaninsa na farko kan juyin mulkin da aka yi a Gabon ranar Laraba, kamar yadda mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya bayyana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin sanarwar da kakakinsa, Mista Ngelale, ya fitar ya ce Shugaba Tinubu yana sa ido sosai kan halin da ake ciki a Gabon bayan kifar da zababɓiyar gwamnati.

Sanarwan ta ce:

"Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na bibiyar abubuwan da ke wakana a Gabon tare da nuna damuwa matuƙa kan halin da ƙasar ta tsinci kanta da kuma yaɗuwar mulkin kama karya a nahiyarmu da muke ƙauna Afirka."
"Tinubu, a matsayinsa na mutum wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare Demokuraɗiyya, yana da yaƙinin cewa mulki ya zauna a hannun mutane na gari, ba a karɓe shi da bakin bingida ba."

Kara karanta wannan

Sojojin Juyin Mulkin Gabon Sun Zayyano Dalilai 4 Da Suka Sanyasu Kifar Da Gwamnatin Kasar

"Kan haka, shugaba Tinubu na aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran shugabannin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Afirka domin samun masalaha da ɗaukar mataki na gaba dangane da mulkin Gabon."

Bugu da ƙari ya ce shugaban ƙasa Tinubu zai tattauna da sauran takwarorinsa da nufin cimma matsaya kan yadda zasu ɗauki matakin magance kwatar mulkin sojoji da ke yaɗuwa a nahiyar Afirka.

Daily Trust ta ce masu juyin mulkin sun bayyana da sanyin safiyar Laraba, inda suka soke zaben ranar Asabar, wanda aka ayyana Bongo ne ya lashe zaben.

"Ku Taimake Ni" Hambararren Shugaban Gabon Ya Fitar da Sako

A wani rahoton kuma Shugaban ƙasar Gabon, Ali Bongo, wanda sojoji suka hamɓarar da gwamnatinsa ya yi kira ga ƙasashen duniya da su kawo masa ɗauki.

A wani faifan bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya, Bongo ya roƙi kasashen da ke ƙawance da ƙasar Gabon su taimaka su kai masa agaji a inda yake tsare.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sojojin Juyin Mulkin Gabon Sun Cafke Dan Shugaba Ali Bongo, Sun Bayyana Dalilansu

Asali: Legit.ng

Online view pixel