Bidiyo: "Ku Taimake Ni" Hambararren Shugaban Gabon Ya Fitar da Sako

Bidiyo: "Ku Taimake Ni" Hambararren Shugaban Gabon Ya Fitar da Sako

  • Hambararren shugaban ƙasar Gabon, Ali Bongo, ya roƙi kasashen duniya da abokanansa su taimaka su kawo masa ɗauki
  • A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Shugaba Bongo ya ce sojoji sun kama shi tare da iyalansa a wurare daban-daban
  • Da safiyar Laraba ne aka wayi gari da sanarwan sojojin ƙasar Gabon, inda suka ce sun soke zaɓen ranar Asabar wanda Bongo ya samu nasara

Gabon - Shugaban ƙasar Gabon, Ali Bongo, wanda sojoji suka hamɓarar da gwamnatinsa ya yi kira ga ƙasashen duniya da su kawo masa ɗauki.

Hamɓararren shugaban na tsare a hannun sojoji biyon bayan juyin mulkin da manyan jami'an sojin ƙasar Gabon suka masa.

Hambararren shugaban ƙasar Gabon, Ali Bango.
Bidiyo: "Ku Taimake Ni" Hambararren Shugaban Gabon Ya Fitar da Sako Hoto: thenation
Asali: Twitter

A wani faifan bidiyo da jaridar The Nation ta wallafa a shafin X watau Tuwita, Bago ya roƙi kasashen da ke ƙawance da ƙasar Gabon su taimaka su kai masa agaji a inda yake tsare.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Maida Martani Kan Sabon Juyin Mulkin da Sojoji Suka Yi a Gabon, Ya Faɗi Mataki Na Gaba

A bidiyon, hamɓararren shugaban Gabon ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ni ne Ali Bongo Ondimba, shugaban ƙasar Gabon, kuma ina miƙa wannan sako ga dukkan abokanmu na faɗin duniya cewa su yi wa mutanen nan magana, sun kama ni tare da iyalaina."
"Ɗa na yana can wani wuri a tsare, matata tana wani wuri daban, ni kuma gani nan a gida. A halin yanzu ina gida kuma babu abinda ke faruwa, ban san halin da ake ciki ba."
"Kuma ina roƙon ku da ku yi magana, ku yi magana, ku ƙara magana, ina godiya a gare ku, na gode."

Juyin mulki a kasar Gabon

Jaridar Premium Times ta ruwaito yadda jami’an soji a Gabon suka karbe mulki a kasar da ke tsakiyar nahiyar Afirka.

A cewarsu, sun kwace mulki a kasar ne saboda zaben da aka gudanar a karshen mako bai dace ba. Sun soke zaben, sun rusa dukkan hukumomin gwamnati tare da rufe iyakokin kasar.

Kara karanta wannan

Sojojin Juyin Mulkin Gabon Sun Zayyano Dalilai 4 Da Suka Sanyasu Kifar Da Gwamnatin Kasar

Shugaba Tinubu Ya Maida Martani Kan Sabon Juyin Mulkin da Sojoji Suka Yi a Gabon

A wani labarin kuma shugaban Najeriya ya maida martani ma farko kan juyin mulkin da Sojoji suka yi a ƙasar Gabon da ke tsakiyar Afirka.

Tinubu ya bayyana matukar damuwarsa kan yanayin da ake ciki na dambarwar siyasa da zaman lafiya a kasar sakamakon hamɓarar da shugaba Ali Bongo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel